Yayin da ya kasnce a ranar 29 ga watan Mayu za a rantsar da zababben Shugaban kasa, Bola Tinubu akwai manyan kalubalen da suke gabansa kafin ya samu nasarar darewa kan karagar mulki.
Daga daga cikin wadannan kalubale ita ce, tsarin karba-karba wurin zaben shugabannin majalisu, wanda an dade ana kai-ruwa-rana a tsaknin mambobin zauren majalisun guda biyu na yadda ake kokarin saka addini da bangarenci ta yadda za a bai wa sashin kudu masu yamma, yayin da wasu ke ganin ya dace a bai wa yankin arewa maso yamma matsayin, saboda yawan kuri’u da zababben shugaban kasa ya samu a wannan yanki.
Haka kuma sababbin mambobin majalisa idanuwansu na kan samun zama shugaban majalisan dattawa, saboda yadda aka zabe su a matsayin ‘yan majalisa a yankunan arewa da kuma na kudu, inda yankin kudu maso gabas ya koko kan yadda bai taba rike wannan kujarar ba. Ana ganin yankin kudu maso kudu ke rige-rige da yankin kudu maso gabas wajen samun mukamin shugabancin majalisan dattawa, domin tabbatar da kirista ya zamanshugaban majalisan dattawa ta yadda za a samu daidaito a tsakanin addinai lasancewa takarar musulmi da musulmi jam’iyyar APC ta yi.
Samun shugaban majalisar dattawa a yankin arewa maso yamma zai haifar da ce-ce-ku-ce, sannan yankin kudu maso kudu da yankin kudu maso gabas ba za su lamunta ba, saboda an zabi shugaban kasa musulmi da mataimakinsa musulmi. Haka kuma mukamin shugaban majalisan wakilai ana kai ruwa rana. Tinubu ne kadai zai iya zaben shugabannin majalisu guda biyu tare da kawo karshen ce-ce-ku-ce kan tsarin karba-karba a wurin raba mukamai da daidaiton addini da kuma cusa ra’ayin addini wajen bayar da mukami.
Haka kuma ana tsammanin zababben shugaban kasa ya yi amfani da sauran kwanakin da suka rage masa ya kafa majalisar ministocinsa domin tabbatar da samun nasara bayan ya gaji Shuagaban kasa. Muhammadu Buhari wanda ya shafe watanni shiga kafin iya zakulo mambobin majalisar minintocinsa bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2015, sannan ana tsammanin Tinubu zai kauce wa fadawa irin wannan kuskuren.
Wani babban kalubalen da Tinubu yake fuskanta shi ne, yadda zai fuskanci cire tallafin man futar wanda za a cire da zai fusata kungiyar kwadugo ta kasa (NLC), wanda suka yi gargadin cire tallafin man. Dokar man nfetur da aka samar a 2022, ta bayyana cewa cire tallafin man da majalisa ta dakatar na tsawon watanni 18, inda zai kare a watan Yuni.
A makon da ya gabata an ji babban sakataren ma’aikatar man fetur, Ambassador Gabriel Aduda cewa an yi la’akari da abubuwa masu yawa wajen tabbatar da cire tallafin mai wanda Tinubu zai fuskanci kalubale, wanda yana cikin alkawarin yakin neman zabe da yadda zai aiwatar da shi ba tare da ya fuskamci bore daga mutane kafin a rantsar da shi.
Zababben shugaban kasa zai kuma fuskanci babban aiki a gabansa wajen tabbatar da sake maido da ingancin rayuwa da zai hada kan ‘yan Nijeriya. A halin yanzu dai, kawunan ‘yan Nijeriya sun rabu ta bangaren akilanci da addini. Hanya daya da zai bi shi ne, tabbatar da adalci da daidaito wajen zaben makarrabansa a majalisar kasa. Haka kuma Tinubu zai fuskanci kalubale wajen wanke kansa kan tuhumar da ake masa a kotunan sauraren karar zabe ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Mista Peter Obi da takwarensa na jam’iyyar PDP, Atilu Abubakar da dai sauransu.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da ya gudana a ranar 25 ga watan Fabrairu, bayan samunkuri’u 8,794,726. Wanda ya doge abokan hamayyarsa da suka hada da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku da takwaransa na jam’iyyar LP, Obi wadanda suka samu kuri’u 6,984,520 da 6,101,533 a jamlace.
A makon da ta gabata ce Tinubu ya bayyana sunayen mutum 13 a matsayin ‘yan kwamitin amsar mulki a ranar 29 ga watan Mayu. Sai dai kuma PDP ta cacceki Tinubu domin bai nada kowa ba daga yankin kudu maso gabas a cikin mutum 13 da ke cikin kwamitin amsar milki.
Ya dai mika sunayen mutum 13 ne a wata wasika da ke dauke da sa hannun sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, wanda ya bayyana sunayen mutum 13 a matsayin wadanda aka hada a cikin kwamitin amsar mulki.
Kwamitin zai fara aiki ne mako guda kafin rantsarwa wanda zai mika mulki ga Tinubu da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima a matsayin shugaban kasa da mataimaki a ranar 29 ga watan Mayu, inda tun da farko aka bayyana sunan Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu da tsohon kwamishinan kudin Jihar Legas, Wale Edun na daga cikin ‘yan kwamitin.yus