• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Marigayiya Hajiya Murja Bara’u Mangal: Uwa Tagari

by Leadership Hausa
3 years ago
Marigayiya Hajiya Bara'u Mangal

Marigayiya Hajiya Bara'u Mangal

Masu iya magana na cewa mai son dan kwarai, ya auri isassa. Wannan falsafa daga kundin hikimomin Malam Bahaushe, ba ma za ta saidu kawai ba ne ga sauran al’ummomi.

Har ma za a iya yin na’am daya bawa da ita. Domin kuwa duk inda ka gadan kirki, daga kuma kowace irin al’umma ya fito, to kuwa babu shakka da ka bincika, zaka samu cewa ya samu tarbiya ta gari.

  • Yadda Za Ki Gane Yanayin Fatarki
  • Yaya Ake Gane Alamomin Mutum Ya Yi Kyakykyawan Karshe?

Kaso mai tsoka kuwa na samun tarbiya ta gari daga uwa ake samunta. Domin kuwa ita ce ke tare da shi, take kuma kula tare da auna kowane irin motsi nasa tun daga kuruciya har girmansa.

Wannan ga kowane gama garin mutum kenan. Ga Alhaji Dahiru Mangal, abin ya zarce haka. Domin kuwa yayarsa Hajiya Hauwa ta tabbatar mani da cewa alakar Alhaji Dahiru Bara’u Mangal da mahaifiyarsa ta zarce duk yadda ake tsammani.

Domin kuwa a kowace rana ta Allah, idan ya fito daga gidansa gidan mahaifiyarsa yake soma zuwa ya gaishe ta.

LABARAI MASU NASABA

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya

Idan kuwa har wata hidima wadda ke da lokaci ta rutsa da shi, kamar daurin aure da makamancinsa, to kuwa idan ma har ya wuce bai samu zuwa ya gaishe ta ba, to kuwa daga can gidanta zai zarce.

Haka kuma, idan ya yi tafiya ya dawo, gidanta ya ke soma zuwa kafin ya wuce gidansa. Sai dai ko idan da daddare ya dawo.

Ba gaisuwa kawai ke kai Alhaji Dahiru Mangal ga mahaifiyarsa ba, har da sauraren bukatunta domin ya biya mata.

Yana kuma jin linzaminta yadda ya kamata. Yana tsayawa cak, inda ta tsaida shi. Ya kuma ruga inda ta aike shi. Ma’ana dai bai hada ta da komai ba. Maganarta ita ce ta karshe. Kuma ko ya takura, huskarsa ba ta nuna takurar.

 Wasu na hasashen cewa wannan ne ma sirrin nasararsa. Ta yadda yake samun nasara ga dukkan abubuwan da ya tunkara a rayuwa.

Malam Abbate wani dattijon Malami a garin Katsina wanda kuma ya rage daga cikin abokan Alhaji Bara’u wato Mahaifin Alhaji Dahiru Mangal ya bayyana mani cewa Alhaji Dahiru Mangal ya gaji wannan kyautatawa da yake yi wa Mahaifiyar tasa ne daga Kakansa Alhaji Tukur, wanda ya kan je ya gaida mahaifiyarsa, wadda ake cewa Done, a kowace rana.

Malam Abbate ya kara da cewa “Shi ma Mahaifinsa Alhaji Bara’u ya kan zo gaishe da wannan tsohuwa da kuma kawo mata abinci. Ta haka ne ma muka saba da juna, har muka zama aminan juna.

Da yake gidanta yana makwabtaka da gidanmu. Don haka, duk lokacin da ya zo ya kan shiga ya gaishe da Shehi (Mahaifinsu).”

An haifi Hajiya Murja Muhammad Dodoa shekarar 1937. Mahaifinta shi ne Alhaji Dodon Kanti.

Ita ce diyarsa ta biyu. Ta yi aure tun tana da shekara goma sha ukku (13) a duniya, a shekarar 1950.

Ta haifi ‘ya’ya takwas, hudu maza, hudu mata. Mazan su ne Alhaji Dahiru Bara’u Mangal (na farko a cikin maza, na biyu a haihuwa) da Marigayi Alhaji Muntari da Alhaji Bishir da kuma Marigayi Alhaji Marwana.

A lokacin da matan sukakasance Hajiya Hauwa (ta farko a haihuwa)da Marigayiya Hajiya Mariya da Hajiya Zulai da kuma Marigayiya Hajiya Nana Bilkisu.

Wato hudu daga cikin su ne ke raye. Biyu maza, biyu mata. Mazan su ne Alhaji Dahiru Bara’u Mangal da Alhaji Bishir Bara’uMangal.

A lokacin da matan suka kasance Hajiya Hauwa Bara’u Mangal da Hajiya Zulai Bara’u Mangal.

Hajiya Murja na daukar nauyin mutane da dama zuwa aikin Hajji da Umra, musamman ma aminanta da ‘yan’uwa da abokan arziki.

Kuma dukkan nauyi take daukewa ba tare da rage komai ga wanda ta dauki nauyinsa. Kusan dukkan tafiya-tafiyen da take yi, musamman ma aikin Hajji da umra tare take yinsu da Babbar kawarta, kuma aminiyarta ta kusa Hajiya ‘Yarbaba.

Marubucin wannan mukala ya jinjina masaa lokacin da wani abokinsa Alhaji Magaji Abdullahi Kankiya ya sheda masa cewa a lokacin da ya je aikin Hajji sun zo filin jirgiza su dawo gida a Jirgin Mad Air sai suka iske Hajiya (mahaifiyar Alhaji Dahiru Mangal) ta riga ta shiga jirgin ita ma za a dawo da ita.

Irin yadda ya ga baki dayan ma’aikatan jirgin na kazar-kazar da ~arin jikin ganin fasinjojin jirgin sun shiga jirgin a cikin gaugawa, domin kada a bata mata lokaci.

Lamarin da ya sa Alhaji Magajin ya sheda irin tsabar girmamawar da Alhaji Dahiru Mangal ke yi wa mahaifiyarsa. Wanda kuma ga shi har hakan ya yi naso ga ma’aikatansa.

Allah Ya jikanta da rahma. Ya girmama lada. Ya kuma sa Jannatul Firdausi ta zama makomarta.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce
Manyan Labarai

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

October 4, 2025
Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya
Rahotonni

Nijeriya A 65: ACF Da Afenifere Sun Yi Hannun Riga Kan Makomar Nijeriya

October 4, 2025
Bashin Karatun Dalibai: Arewa Maso Yamma Ce Kan Gaba Wajen Cin Gajiyar Shirin
Rahotonni

Bashin Karatun Dalibai: Arewa Maso Yamma Ce Kan Gaba Wajen Cin Gajiyar Shirin

October 3, 2025
Next Post
Muna Bukatar Tallafin Gwamnati Don Bunkasa Noma A Garin Gwanda -Mai Unguwa Yahuza

Muna Bukatar Tallafin Gwamnati Don Bunkasa Noma A Garin Gwanda -Mai Unguwa Yahuza

LABARAI MASU NASABA

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati

October 9, 2025
An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba

October 9, 2025
Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.