ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Martanin Kwankwaso Ga Kawu Sumaila Da Sauran Masu Ficewa Daga NNPP

by Abubakar Sulaiman
7 months ago
Kwankwaso

Jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi kakkausar suka ga ‘yan siyasar da suka sauya sheƙa bayan samun goyon bayan jama’a, inda ya kira halin hakan a matsayin “babban laifin siyasance.” Ya bayyana hakan ne a wajen karɓar sabbin mambobin jam’iyyar daga Takai a gidansa da ke Kano.

Kwankwaso ya mayar da wannan martani ne bayan wasu manyan ‘yan jam’iyyar da suka koma APC, ciki har da Sanatan Kano ta Kudu Abdurrahman Kawu Sumaila da ɗan majalisar wakilai Kabiru Alhassan Rurum. Ya yi tir da waɗanda suka samu ragamar mulki ta hanyar ƙuri’un jama’a a jam’iyyarsu amma sai suka juya su ga abokan adawa.

“Wannan shi ne mafi girman cin amana a tsarin dimokuraɗiyya. Ban san wani laifi mafi girma ba fiye da lokacin da talakawa suka zaɓe ku don gujewa mayaudara, amma sai ku juya ku shiga cikinsu. Da sun sani, da ba su zaɓe ku ba,”

in ji shi.

ADVERTISEMENT

Ya kuma yi gargaɗin cewa duk wanda ya yi yunƙurin kai hari kan tsarin Kwankwasiyya zai fuskanci tsayin daka mai ƙarfi. Daga nan yayi kira ga mabiyansa da su ci gaba da faɗaɗa jam’iyyar ta hanyar jawo sabbin mambobi daga matakin gundumomi.

Kwankwaso ya jaddada cewa Kwankwasiyya yunƙuri ne na hidima ga jama’a ba na neman riba ba. Ya yi ishara da zaɓen Kano ta Kudu inda ya ce wasu sun sayar da ƙuri’unsu kan taliya da ₦2,000, amma talakawan Kano sun tsaya tsayin daka ba su sayar da ƴancinsu ba.

LABARAI MASU NASABA

Cikin Sauƙi Na Yanke Shawarar Komawa APC – Gwamna Fubara

Ba Zan Taɓa Komawa Jam’iyyar APC Ba — Abaribe

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Siyasa

Cikin Sauƙi Na Yanke Shawarar Komawa APC – Gwamna Fubara

December 18, 2025
Ba Zan Taɓa Komawa Jam’iyyar APC Ba — Abaribe
Siyasa

Ba Zan Taɓa Komawa Jam’iyyar APC Ba — Abaribe

December 16, 2025
El-Rufai Ya Ƙaryata Rahoton Goyon Bayan Yanki Ko Wani Mutum A Zaɓen 2027
Siyasa

El-Rufai Ya Ƙaryata Rahoton Goyon Bayan Yanki Ko Wani Mutum A Zaɓen 2027

December 15, 2025
Next Post
Wayar Salula Na Dab Da Kai Mu Wutar Jahannama

Wayar Salula Na Dab Da Kai Mu Wutar Jahannama

LABARAI MASU NASABA

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025
An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.