“Nijeriya ta sake fuskantar babbar gazawar a fannin tsaro yayin da fursunoni 16 suka tsere daga Gidan Yari a Keffi, da sanyin safiyar Talata. Wannan lamari ya sa fursunoni sun rinjayi jami’an tsaro, suka jikkata mutum biyar, daga cikinsu biyu suna cikin mummunan hali kuma suna karbar magani a asibitin gwamnati.”
Gidajen yarin Nijeriya ya sha fama da yawan tserewar fursunoni tare da cunkoson wadanda ake jiran kisa.
- UNICEF Na Neman Naira Biliyan 240 Don Ayyukan Agaji A Nijeriya
- JAMB Ta Kaddamar Da Kwamitin Bincike Kan Satar Jarabawa
Tsawon shekaru, wadannan matsalolin sun bayyana raunanan tsare-tsare daga gazawar tsaro zuwa matsalolin shari’a, lamarin da ya haifar da tambayoyi kan tsaron jama’a da bukatar gyara hukumomi.”
Daga yawan tserewar fursunoni zuwa gazawar na’urorin tsaro, jami’an tsaron gidajen yari a Nijeriya ba sa sauke hakkin da ya rataya a wuyansu. Wannan rahoton ya yi nazari mai zurfi kan tsarin gyaran hali da ke rushewa, inda ma fiya hatsarin fursunoni suke samu ’yanci.
Abin ban sha’awa, duk da yawan tserewar fursunoni da aka samu cikin shekaru 10 da suka gabata, jaridar LEADERSHIP Weekend ta ruwaito cewa akwai wadanda ke jiran kisa da suka tsere a lokacin wadannan balahira.”
Tserewar fursunoni a gidan yari na Abuja ya dauki sa’o’i 3.
Lokacin da ’yan ta’adda dauke da muggan makamai suka afka wa Gidan Yarin Kuje na Abuja a ranar 5 ga Yuli, 2022, sun kwashe kusan sa’o’i uku suna yawo a farfajiyar gidan, gidan da aka ambata shi a matsayin mafi tsaro a Nijeriya, kuma an yi hakan ba tare da kawo wani dauki ba, kana kyamarori suka kasa gano su, sannan babu jami’in da ya kalubalance su.
Lokacin da komai ya lafa, an gano cewa fursunoni 879 sun tsere, ciki har da wasu 64 da ake zargin ’yan Boko Haram ne da kuma fursunoni 36 da suke jiran kisa.
Harin, wanda daga baya ISWAP ta dauki alhakin kaiwa, wannan harin ba wai abin kunya ne kawai ga kasa, ya zama wata firgitarwa ce, cewa gidan yari mafi karfin tsaro ma ya raunana, wannan ba karamin lamari ne mai tayar da hankali ba.
Sauran manyan abubuwan da suka faru a Owerri (2021), Benin/Oko (2020), Jos (2021), Agodi (2012), da Kabba (2021) sun samu yawan fursunonin da suka tsere, amma babu wanda aka tabbatar daga cikin masu jiran kisa ne.
Sau da yawa ’yan Nijeriya kan dauka cewa gidajen yari na da tsauraran matakan tsaro kamar na Kuje (Abuja), Kirikiri (Lagos), da Port Harcourt an karfafa musu tsaro sosai don tinkarar kowace barazana daga ciki ko wajensu.
Amma tserewar fursunoni da dama sun bayyana gaskiyar wani lamari mai muni: wadannan wuraren da wasu fiye da suka shafe fiye da shekara 60 da kafuwa, suna fama da karancin kudi, tsofaffin tsare-tsare, da kuma manyan gibi a tsaro.
A batun Kuje, wakilinmu ya gano cewa duk kyamarori na CCTB guda 15 ba sa aiki a lokacin harin.”
Wata majiya tushe ta ce kararrawa ba ta yi amo kwata-kwata. An kuma ce an sami tangarda a katangar da ke kewaye da wurin. Abin da ya fi tayar da hankali ma shi ne: jami’an tsaro dauke da makamai guda hudu ne kawai a wurin lokacin da ’yan bindiga kusan 100 suka kai hari.
Wani babban jami’in Hukumar Gyaran Hali ta Nijeriya (NCoS) da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, ‘Babu wata na’urar CCTB da take aiki, babu wata kararrawa da ta yi amo. Komai ya tsaya. Abin da muke da shi shi ne gidajen yari da ke aiki da tsarin shekarun 1990 a cikin yanayin barazana a 2025.’”
Jaridar LEADERSHIP Weekend ta rubuta cewa duk da cewa Hukumar Gyaran Hali ta Nijeriya na karbar kudaden gwamnatin tarayya don samar da kayan tsaro, bayanan ciki da kuma bincike sun nuna gazawa wajen sanyawa ko kula da na’urorin sa ido na zamani a manyan wurare.
Lokacin da aka tambayi dalilin da ya sa kyamarori na CCTB da kararrawa ba sa aiki a wasu gidajen yari, NCoS ta danganta hakan da: ‘karancin kasafin kudi, jinkirin hanyoyin saye, da kuma lalata kayan aiki da fursunoni suka yi a lokacin tashin hankali a baya, wanda ya shafi daidaiton tsarin sa ido namu. Muna aiki tare da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da hukumomin tsaro domin magance wannan matsala.
Sai dai, masana tsaro sun yi jayayya cewa rashin karfafa mulkin siyasa da cin hanci su ma suna taka rawa a cikin matsalar. ‘Ana sayen kayan sa ido amma ba a saka su. Ana bayar da kwangila amma ba a kammala ta. Babu wanda ake dora wa alhaki,’ in ji wani tsohon jami’in Hukumar Tsaro ta Kasa (DSS), rundunar ’yansandan boye ta Nijeriya.”
Ba Kuje kadai ne kadai lamarin ya faru ba.
Abin ya zama kamar al’ada, domin fiye da fursunoni 7,200 ne suka tsere daga gidajen yarin Nijeriya tsakanin shekarar 2019 zuwa 2025 a wadannan lokuta, Benin (2020), Jos (2021), Kabba (2021), Owerri (2021), babu tsarin sa ido da yake aiki, jami’an tsaro da ke bakin aiki sun gaza, kuma babu wata amsa ga tambayoyi game da faruwar al’amuran.
Har yanzu, a cewar bayanan da ake da su, adadin fursunonin da ake jiran kisa da suka yi nasarar tserewa babu labarinsu, kada ma na Kuje su ji labari, inda har yanzu ba a tabbatar da tserewarsu ba amma kuma ba a san inda suke ba.”
Wata babbar majiya a hedkwatar Hukumar, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa wakilinmu cewa an gano wuraren da fursunonin da suka tsere suke da kuma gibin tsaro daban-daban da aka samu.
Ta ce a shekarar 2022, fursunoni 879 sun tsere daga Kuje (Abuja) sakamakon rashin CCTB da kararrawa, abin takaici da ya jawo mutuwar jami’an tsaro dauke da makamai hudu.
Ta kuma ce a shekarar 2021, fursunoni 240 daga cikin 266 sun tsere daga Kabba Jihar (Kogi), inda aka kashe jami’an tsaro biyu bayan an tarwatsa kofar shiga.”
A shekarar 2021 a Owerri (Jihar Imo), fursunoni 1,844 sun tsere, wanda aka danganta da hare-haren daga waje lamarin da ya fi karfin jami’an tsaro. Haka kuma a shekarar 2020 a Benin/Oko (Jihar Edo), fursunoni 1,993 sun tsere lokacin da aka mamaye gidan yari a yayin zanga-zangar #EndSARS.
Majiyar ta kara da cewa yayin da lamura ke kara dagulewa, talakawa ne ke daukar kasada. Al’umman da ke kusa da wuraren da fursunonin tserewa na rayuwa cikin tsoro. Al’amjuran shari’a na kara samun kom-baya a Nijeriya.
Wata babbar majiya a hedkwatar Hukumar ta gano rashin ladabtar da jami’ai da kuma ‘kofar juyawa’ a matsayin wani bangare na matsalar.
‘Ka duba ta wannan hanya,’ in ji shi, ‘duk da yawan tserewar fursunoni, babu babban jami’i da aka gurfanar saboda sakaci wajen aiki.
An kafa kwamitocin bincike, an tattara rahotanni, gami da yin alkawura, duk da haka matsalolin suna nan daram: jami’an da ba su da isassun kayan aiki, karancin kudi, da kuma rashin walwala, wadannan duk hanyoyi ne da za su iya zama dalilan gazawa.’”
Jaridar LEADERSHIP Weekend ta ruwaito cewa ko da yake Hukumar Kula da Gidajen Yari (NCoS) ta sha yin kira a ba ta karin kudi kuma a zamanantar da ita, ciki har da amfani da na’urar tantance bayanai ta zamani (biometrics), kulawa ta hanyar kwamfuta (AI-powered surbeillance), da tsaro na bindigogi a kowane lokaci cikin awa (24/7), ba a ga wani canji a zahiri ba.
Wani kwararren masanin tsaro, Mista Uto-Obong Edwok, ya bayyana cewa sai an dauki gidajen yari a matsayin muhimman gine-ginen kasar, kuma sai an rufe gibin tsaro tare da tabbatar da kulawa, idan ba haka ba, tsaro a gidajen yari “za su ci gaba da kasancewa suna a kadai, ba gaskiya ba.
Ya ce, “Abin da ke sanya gidan yari ya zama ‘mai tsaro kwarai’ shi ne kasancewarsa a (24/7) ana tsare shi da sintirin masu dauke da bindigu. Ya kamata ya kasance da shingaye biyu tare da na’urorin gano motsi, hasken lantarki, da kyamarorin sa ido.
“Ya kamata a sami wuraren da ba kowa zai iya shiga ba (restricted access zones), kuma a rika sarrafa motsin fursunoni. Ya kamata a sami wutar lantarki gami da kararrawa da tsarin tsaro, amma abin takaici shi ne a Nijeriya, da yawa daga cikin gidajen yari da ake ba su da rabin wadannan ka’idoji.”
Mun nemi jin ta bakin Jami’in hulda da jama’a na Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Nijeriya (NCoS), DCC Umar Abubakar, amma saboda matsalar hanyoyin sadarwa lamarin ya ci tura.
Hatta sakonnin kar ta kwana da muka aika ba su samu isa gare shi ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp