A kwanakin bayan ne gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani sabon tsarin noma shinkafa na kasa na shekara 10, inda masu ruwa da tsaki a a fannin suka yi amfani da damar don karfafa tsarin, yadda manoma za su ci gajiyarsa.
Wata gidauniyar bunkasa noma ta duniya da ake kira ‘Syngenta’, ta yi hadin gwiwa da shirin noma na (SFSA) don bunkasa shi yadda za a samun riba.
Haka kuma yau, gidauniyar ta kuma yi hadaka da kamfanin Derftdan don yin nomanta yadda za a samun riba a kasar nan.
A jawabinsa a wajen taron bitar wanda aka yi a Abuja, shugaban sashin bunkasa noma Robert Berlin ya bayyana cewa, an shirya taron bitar ne domin a duba irin nasarar da aka samu a cikin shirin na SFSA, tare da samar da wani kundi don samar da gudummawa wajen karfafa aikin noma yadda za a samun riba mai yawa.
Berlin ya ce, wannan taron bitar ya zo ne bayan gwamnatin tarayya tk kaddamar da dabarun tsarin na aikin noma na kasa don samun riba ta shekaru 10,musamman domin a samar da wadatacciyarta a kasar nan, inda kuma ya yaba wa mahalarta taron kan amsa gayyatar halartar taron.
Shi ma a nasa jawabin, ministan noma da raya karkara, Dakta Mohammed Mahmood Abubakar, ya jinjina wa gidauniyar kan gagarumar gudunmawar da ta bayar don karfafa tsarin na aikin noma don samun riba.
Ministan wanda Darakta a ma’aikatar, Bashir Umar ya wakilta a gurin taron ya bai wa mahalarta taron tabbacin gwamnatin tarayya don tallafa wa, musamman kananan manoman shinkafa, mussman domin a cike gibin da ake da shi na noman shinkar domin samun riba.
Abubakar ya yi kira ga mahalarta taron da su yi amfani da ilimin da suka samu a taron bitar tare da kuma wanzar da mastayar da aka cimma a gurin taron.
Shi kuwa manajan gidauniyar Isaiah Gabriel a nasa jawabin a gurin taron ya bayyana cewa, gidauniyar da kuma kamfanin Derftdan Resources ne, suka gudanar binciken domin yin nazari akan noman na shinkafar da sarrafa ta da kuma sayar da ita domin samun riba.
Gabriel ya ci gaba da cewa, nanufar mu ita ce, domin a gano kalubalen da kuma gibin da ake da shi don a karfafa tsarin na aikin noma don samun riba.
Ya sanar da cewa, ana iya Nijeriya za ta iya rungumar wannan tsarin domin a karfafa aikin noma shinkafar da kuma sarrafa ta.
A cewar Gabriel, manoma 2,249 ne suka goyi bayan gudanar da wannan binciken wanda kuma aka gudanar a jihar Koros Ribas da Neja da Edo Jigawa da Kebbi da Ebonyi da Kano da kuma Nasarawa.
Shi ma a jawabinsa a wajen taron wani babban jami’in tuntuba a fannin noma don samun riba Mista Richard Ogundele ya sanar da wasu gibin da aka samu a fannin noman shinkafa don samun riba.
A cewar Mista Richard damar da ake da ita don bunkasa noman shinkafar don samun riba, ta karade daukcin fadin kasar nan.
Ya kara da cewa, akwai bukatar a kara bunkasa noman shinkafar don samun riba a Nijeriya, musamman ga hanyar samar da kayan nomanta na yamani da samar da ingantaccen Iri.
Ya bayyana cewa, mutukar aka samar da ingancciyar shinkafar an kammala komai da ya kanata, inda ya kara da cewa, matukar aka mayar da hankali akan tsarin nomanta, hakan zai kara taimaka wa wajen nomanta a kasar nan har a kuma fitar da ita zuwa kasuwar duniya.
Mista Richard ya kara da cewa, masu ruwa da tsaki a fannin sun kuma tattauna akan matsalolin da fannin na noman shinkafar don samun riba ke fuskanta a kasar nan, inda suka bayyana cewa, akwai bukatar a yi amfani da fasahar zamani don a shawo kan matsalar, musamman domin a kara bunkasa nomanta a kasar nan.
Sauran masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun hada da, kungiyar manoman shinkafa ta kasa da cibiyar gudanar da bincike a kan amfanin gona da sauransu.