A zamanta na Farko cikin wannan shekarar Majalisar Masarautar Zazzau karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR ta amince da ranar Jumma’a, 12 ga watan Janairu, 2024 a matsayin ranar da za a gudanar da nadin sabon Magajin Garin Zazzau da Baraden Zazzau da kuma Gado Da Masun Zazzau.
Wadanda za a nada a wannan ranar sun hada da Baraden Zazzau Alhaji Mu’azu Nuhu Bamalli wanda ya samu ci gaba zuwa Magajin Garin Zazzau. Ita dai wannan sarauta na Magajin Gari tana daya daga cikin sarautun ‘ya’yan Sarki a Masarautar Zazzau wanda Alhaji Mu’azu Nuhu zai maye gurbin ‘Dan uwansa ne Marigayi Magajin Garin Zazzau Ambasada Mansur Nuhu Bamalli wanda Allah Yai wa rasuwa a cikin watan Oktoban shekaran da ta gabata.
- An Kashe Sama Da Mutane 100 A Harin Bam A Iran
- Juyin Mulki: Faransa Ta Rufe Ofishin Jakadancinta Na Nijar
Har ila yau, Alhaji Aliyu Nuhu Bamalli, Shugaban Ma’aikata a Masarautan Zazzau za a nadashi a matsayin sabon Baraden Zazzau da kuma Alhaji Aminu Musa Hassan wanda za a nada a matsayin sabon Gado Da Masun Zazzau. Alhaji Aminu dai ya gaji Mahaifinsa ne wato Marigayi Alhaji Musa Hassan Gado Da Masun Zazzau wanda Allah Yai a rasuwa cikin watan Nuwamba nw Shekaran da ta gabata.
Kamar yadda Majalisan Masarautar Zazzau ta amince, za a gudanar da nade-nade ne bayan idar da sallar Jumma’a a wannan ranar.