Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTAUNAWA

Mashin Ɗina Na Sayar Don karɓan Shirin Gwamnati Na Noman Shinkafa – Salihu

by Tayo Adelaja
October 23, 2017
in TATTAUNAWA
4 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Wakilinmu MUHAMMAD AWWAL UMAR ya samu damar tattaunawa da Hakimin Tunga Mata, ALHAJI SALIHU, inda ya nuna farin cikinsa kan irin nasarar da suka samu duk da rashin tallafin gwamnati. Ga yadda hirar ta kasance

Da farko zamu so jin sunan ka.

Sunana Alhaji Salihu Ango, ni ne hakimin Tungan Mata da ke yankin ƙaramar hukumar Yauri ta nan jihar Kebbi.

 

To da farko mu al’ummar ƙasar Tungan Mata muna godiya ga gwamnatin tarayya bisa jagoranci Malam Muhammadu Buhari kuma muna godiya ga mai girma gwamnan jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu. Domin lokacin da gwamnati ta ƙaddamar da wannan shirin mu dai gare mu nan ba mai wani jarin yunƙurawa, a matsayina na shugaban al’umma kuma Hakimin yankin nan sai na ga ya kamata in bada misali, da farko ina kiwon nagge sai na sayar da ita akan dubu ɗari da saba’in da biyar, akwai mashin ɗin da na saye dubu ɗari biyu da goma sha bakwai sai na karyar da shi naira dubu ɗari biyu, jimilan na samu kuɗin jarin noma dubu ɗari uku da saba’in da biyar da su na aikin noman shinkafa a shekarar bara.

 

Bayan ka zuba waɗannan kuɗaɗe akwai wani abu da ya biyo baya

To, lallai ka san mu mutanen karkara komai na da sauƙi nan gare mu duk da cewar ita gwamnati ba ta ba mu tallafin komai ba, bayan an kawo anfani gona gida na samu buhun shinkafa ɗari biyu har da wani abu haka.

 

Kana nufin shinkafa kaɗai ne ka samu wannan zunzuruntun alheri haka

Ƙwarai kuwa, nan a yankin da ni ke mu manoman shinkafa mun yi ƙungiya da nufin idan an zo bada tallafi ko rance zamu samu, mu ɗari da saba’in da biyar ne ke cikin wannan ƙungiya amma dai daga ita gwamnatin tarayya har ta jiha ba wadda ta ba mu tallafi koda sisin kwabo kuma dukkanin mu da ƙarfinmu mun samu alheri mai yawa da wannan ƙuduri na gwamnati akan noman shinkafa duk kuwa cewar ba a ba mu tallafin komai ba, amma dai mun yaba domin ƙudurin ita gwamnatin ne ya ƙara mana himma.

Ganin ita jihar ku ta Kebbi tana ɗaya daga cikin jahohin da aka ware dan bunƙasa noman shinkafa, kana ganin za ku iya baiwa maraɗa kunya kuwa

Maganar baiwa maraɗa kunya an ba su wa kuwa, domin idan yau gwamnatin tarayya da ta jiha zasu iya haɗa kai, ina tabbatar ma ka cewar jihar Kebbi kaɗai na iya wadata ƙasar nan da abinci ba sai an shigo da shi daga waje ba. Sannan mu manoman da gwamnati za ta iya samar mana da wani tsari na tallafawa mu manoman ta hanyar kawo ‘yan kasuwa masaya, sannan kuma a riƙa ba mu tallafi na irin shinkafa na zamani da kuma takin zamani wanda zai taimakawa noman na mu ina tabbatar maka da mun ci galaba akan talaucin da ke damun al’umma.

 

Yanzu a nan yankin na ku na Tungan Mata ko za ka iya ƙididdige adadin manoman shinkafa da cushe a nan

Ai ƙasar tana da yawa sosai, misali idan ka fito daga Giron Masa, manoman shinkafa ne, idan ka ƙarabo nan gaba zuwa Nasarawa manoman shinkafa ne haka kuma idan ka shigo nan lungun na Tungan Mata manoman shinkafa ne yankin ƙaramar hukumar Yauri kaɗai idan da gwamnatin jiha za ta mai da hankali akan noman shinkafa kaɗai ina tabbata maka da an ga alfanun hakan, amma maganar yawan manoma kan ba su ƙirƙuwa domin daman mu nan manoman ne, nomar ita ce babba sana’a wajen mu.

 

Yanzu gaya shinkafar da aka sanya bana ta taso ko kana ganin duk da irin wannan rashin tallafin noman ku na bana zai kai na bara kuwa

Kai duba fa, nan cikin gonar ne. Noman da nayi bara bai kai na bana ba, ka ga ke nan idan zan samu buhu ɗari biyu na shinkafa a bara na bana ko lallai zai wuce nan amma dai ina sa ran bana kam kila sai na samu sama buhu ɗari uku dan yanzu jarin noma ya samu.

 

Mai girma hakimi, ganin ku ne Iyayen ƙasa kuma Iyayen al’umma, me za ka cewa manoman ƙasar ka

Ba ma ni ba, ina yabawa da shirin gwamnatin tarayya na farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar nan ta hanyar noma wanda tun farko da shi aka tubalin ginin tattalin arzikin ƙasar, na biyu ina yabawa sarakuna Iyayen ƙasa musamman yadda suka tashe tsaye wajen yekuwa ga al’umma na a koma gona, na uku ita kan ta gwamnatin jiha da ba ta aminta da muradin gwamnatin tarayya ba da ba mu samu walwalar da muke samu ba yanzu. Kamar yadda ni ke baiwa al’ummar ƙasar Tungan Mata shawara ko yaushe akan kafa ƙungiyoyin manoma suma sauran yankuna ina ba su irin wannan shawarar, domin idan akwai ƙungiya duk lokacin da ita gwamnati ta tashi yin alheri da ƙungiyoyin nan ta ke anfani.

SendShareTweetShare
Previous Post

Burinmu Waɗanda Muka Horas Su Dogara Da Ƙafafunsu – Tugana

Next Post

Ambaliyar Ruwa Ta Taimaka Wajen Yaɗuwar Ƙyandar Biri ­­­— Masana

RelatedPosts

Har Yanzu Babu Sabuwar Kwalta Ko Kwalbati A Garin Giwa – Kwamred Alkurkawee

Har Yanzu Babu Sabuwar Kwalta Ko Kwalbati A Garin Giwa – Kwamred Alkurkawee

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Daga Idris Umar Game da more romon dimukradiyya da wasu...

Zaman Lafiya

Marasa Son Tabbatuwar Zaman Lafiya A Nijeriya Ke Sukar Furucin Gwamna Bala Kan Fulani, Inji Ladan Salihu

by Muhammad
2 weeks ago
0

DAKTA LADAN SALIHU Shi ne shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar...

Giratuti

Mun Samar Da Daftarin Cigaba Na Shekara 10 Ne Domin Kafa Harsashin Inganta Rayuwar Gombawa –Gwamna Inuwa

by Muhammad
2 weeks ago
0

ALHAJI MUHAMMAD INUWA YAHAYA Shine gwamnan jihar Gombe, a wani hira ...

Next Post

Ambaliyar Ruwa Ta Taimaka Wajen Yaɗuwar Ƙyandar Biri ­­­— Masana

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version