’Yan luwadi da masu fyade 369 ne dubunsu ta cika ta Jihar Katsina a shekarar 2023 da muka yi bankwana da ita.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Aliyu Abubakar-Musa, ya ce ’yan luwadin da masu fyaden suna cikin masu laifi 1,627 da rundunar ta kama a jihar a shekarar.
- Tinubu Ya Bukaci Ma’aikatu Su RIka Fitar Da Rahoton Kasafin Kudi Duk Wata
- Kakakin MOFA: Abin Da Duniya Ke Bukata Shi Ne Hadin Kai
Ya bayyana cewa rundunar ta kuma cafke mutane 176 kan aikata laifin kisa da kuma ’yan fashi da makami 258.
Abubakar-Musa ya ce runduar ta kashe ’yan bindiga 17, ta ceto mutum 171 da aka i gakuwa da su, da wasu 67 daga hannun masu safara bil’Adama.
cewarsa, jami’an rundunar sun kwato bindigogi 12 kirar AK 47, harsasai 1,500, dabbobi 700, da motoci 12 da miyagun kwayoyi iri-iri daga hannun ’yan bindigar da suka shiga hannu.
Babban jami’in ya shaida wa manema labarai cewa wadanda aka gurfanar a kotu kan zarin aikata manyan laifuka sun kai 855, daga cikin 938 da aka samu a jihar a 2023.
Ya bayyana cewa nasara ta samu a sakamakon hadin dan da ke tsakanin rundunar da sauran hukumomin tsaro da ke aiki.
Da haka ya shawarci masu shirin aiakata laifi da su sauya tunani ko kuma su yaba wa aya zaki a hnunn rundunar.
Daga nai sai ya yi kira ga al’ummar jihar Katsina da su ba wa rundunar da sauran hukumomin staro hadin kai, domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.