A Spain ko kuma Andalus, masu zanga-zanga sun yi cunkoso a Barcelona domin nuna adawarsu da shirin zaɓen raba gardama kan ɓallewar yankin Catalonia daga ƙasar ko kuma akasin haka, yayin da ake shirin kaƙa ƙuri’ar a jiya Lahadi. Kotun kundin tsarin mulkin ƙasar ta ba da umurnin jingine zaɓen, lamarin da ya sa gwamnatin tarayya ta Andalus ta ayyana shi a matsayin haramtacce.
Hukumomin Spain sun ce sun rufe cibiyoyin zaɓe da dama sannan sun karɓe ƙuri’un, sai dai duk da haka hukumomin yankin na Catalonia sun yi gaban kansu wajen gudanar da zaɓen, inda suka dasa akwatunan zaɓen a wasu cibiyoyi.
Wani babban jami’an tsaron ƙasar ya ce, sun yi nasarar rufe aƙalla rumfunan zaɓen sama da 2300, da aka tanadar. Ya kuma ƙara da cewa hukumomin ƙasar ta Spain sun yi nasarar ƙwance wata fasahar zamani da za a yi amfani da ita, wajen ƙidayar ƙuri’u, matakin da ya ce zai tilasta dakatar da zaɓen na raba gardamar ɓallewar yankin na Catalonia daga Spain.
Sai dai kuma magoya bayan ganin ƙallewar yankin na Catalonia daga ƙasar Spain, sun yi ƙememe kan dokar da gwamnatin ƙasar ta kafa na hana zuwa cibiyoyin kaƙa ƙuri’a. Rahotanni bayyana cewar tuni wasu daga cikin masu fafututar neman ɓallewar yankin Catalonia ƙin suka fara kaƙa ƙuri’ar raba gardama don tabbatar da cikar burinsu.