Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf ta bayyana cewa batagari sun sace takardun shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje tare da lalata kayan da kudinsu ya kai sama da naira miliyan dubu daya.
A cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na gwamnatin jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ruwaito cewa gwamnan yayi Alla-wadai da abin da bata garin suka yi.
- Matatar Dangote Ta Musanta Kayyade Farashin Man Fetur A Kan ₦600 Kan Kowace Lita
- Cinikin Hajojin Da Ba A Gama Sarrafa Su Ba Tsakanin Sin Da Afirka Ya Karu Da Kashi 6.4 A Watanni Bakwai Na Farkon Bana
Sanarwar ta bayyana cewa shiga cikin kotun da farfasa kayan ciki wasu marasa kishin jihar ne suka kitsa domin sace takardun shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan da iyalansa da kuma masu taimaka masa.
Gwamnan ya kuma bayar da umarnin fara gyaran kotun nan take inda kuma ya yi wa alkalin alkalai ta jihar, Dije Aboki da manyan alkalan kotun jaje bisa wannan ibtila’in da ya afkawa kotun.
Idan baku manta ba, a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a fadin Nigeria baki ɗaya, an lalata kaya tare da sace kayan ƴan kasuwa a wurare daban daban na jihar Kano, ciki har da shiga ginin sakatariyar Audu Baƙo inda aka farfasa motoci da sace kayayyakin aiki.
Alhaji Abba Kabir ya yi kira ga matasa a jihar da su daina bari ana amfani da su wajen tayar da hargitsi, a maimakon hakan, su mayar da hankali wajen neman sana’o’in hannu domin samun kyakkyawar makoma tare da jaddada cewa, gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano.