Wata malama mai suna Joy Eze, a ranar Alhamis ta maka mijinta Nuel Chukwu a gaban kotu a Abuja, saboda ya ki cin abincin da take dafawa, saboda yana zargin tana son sanya masa guba.
Misis Eze wacce ke zaune a yankin Jikwoyi a Abuja, ta yi korafi ne a cikin takardar neman raba aure da ta kai wa Chukwu.
- Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane Fiye Da 130 Cikin Wata Biyu A Nijar
- Kowa Ya Yi Da Kyau Zai Ga Da Kyau
“Ba zan iya ci gaba da zama a karkashin wannan mutumin ba. Ya daina cin abincina, lokacin da na tunkare shi kan batun, ya ce yana sane da shirina na son kashe shi.
“Ya kuma gaya wa danginsa cewa idan ya mutu a kama ni,” in ji ta.
Ta kuma shaida wa kotun cewa Chukwu ya juya tunanin yaranta.
“Mijina ya ci gaba da gaya wa yarana munanan abubuwa game da ni. Ya ce musu ni karuwa ce. Ya shaida musu cewa duk kayan da nake sawa da takalmi masoyana ne ke siya min,” in ji ta.
Ta roki kotun da ta raba aurenta da shi kuma ta ba ta rikon ‘ya’yanta.
Wanda ake karar direban babur mai kafa uku, wanda ya halarci kotun, ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa.
Alkalin kotun, Labaran Gusau, ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 21 ga watan Satumba 2022, domin ci gaba da sauraren karar.