A kwanakin baya ne mahukuntan kasar Sin, suka fitar da wani kundin bayani, mai kunshe da matakan yayata ilimin kimiyya tsakanin al’ummar kasar, matakan da ake fatan za su taimaka wajen ingiza kwazon al’umma a fannin samar da ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire.
Ofisoshin sakatariyar kwamitin tsakiya na JKS, da majalisar gudanarwar kasar ne suka fitar da kundin cikin hadin gwiwa. Kundin ya kuma karfafa muhimmancin hade matakan yayata ilimin kimiyya, da fannin kirkire kirkiren kimiyya da fasaha.
Kana ya fayyace sassa daban daban game da irin matakan da za a aiwatar domin cimma nasarar da aka sanya gaba.
An tsara cewa, ya zuwa shekarar 2025, za a kai ga fafada ayyukan yayata ilimin kimiyya tsakanin al’umma, inda masu bincike za su kara taka muhimmiyar rawa, wajen yada ilimin kimiyya, ana kuma sa ran adadin al’ummar kasar Sin masana ilimin kimiyya zai haura kashi 15 bisa 100, kana adadin ’yan kasar masu maida hankali ga kimiyya da kirkire-kirkire zai yi matukar karuwa.
Kundin ya kara zayyana cewa, ya zuwa shekarar 2035, ana sa ran adadin al’ummar kasar Sin masu sani game da ilimin kimiyya zai kai kashi 25 bisa dari, yayin da yawaitar masu fahimtar kimiyya zai taka muhimmiyar rawa wajen samar da ingantaccen ci gaba.
Abin da ke kara bayyana cewa, kimiya da fasahar kirkire-kirkire sun kasance muhimman tushen ci gaban kasa a wannan zamani.
Wannan na zuwa ne, yayin da aka yi nasarar kammala bikin baje kolin cinikayyar hidima na kasa da kasa na kasar Sin na wannan shekara.
Yayin bikin na kwanaki 6, an gudanar da jigon taruka sama da 100 da gabatarwa da shawarwari fiye da 60, wanda ya cimma jimillar nau’o’in sakamako 1,333 da suka hada da hada-hadar kasuwanci, da saka jari, da gabatar da dabaru da yarjeniyoyin hannayen jarin kirkire-kirkire a sauransu. A bana yawan mahalarta taron ya zarce dubu 250.
Sabanin yadda a mafi yawan lokuta irin wadannan bukukuwan baje koli ke karewa a matsayin wani taro na shan-shayi, bikin CIFTIS na bana, ya zama mafi girma a bangaren ma’auni da kimar bunkasa duniya.
Ya kuma janyo hankalin manyan kamfanoni 507 dake sahun gaba a duniya, inda suka halarci bikin a zahiri.
A karon farko an gabatarwa kamfanoni da cibiyoyi sabbin samfuran fiye da 100 da sabbin fasahohi na nasarori a fannonin kwaikwayoyin tunanin dan-Adam.
Duk da cikas din da ake fuskanta a kokarin da ake na dunkulewar duniya gami da rikice-rikice da ake fuskanta a sassan duniya, bikin na CIFTIS ya kara samun mahalarta, saboda wasu muhimman dalilai, da suka hada da yadda kasuwar kasar Sin take jawo hankali sosai, da yadda bikin ya zama muhimmiyar alamar yadda kasar Sin take kara bude kofa ga kasashen ketare, zurfafa hadin gwiwa, da ba da jagora kan yin kirkire-kirkire, da nuna aniyar kasar Sin ta kara azama kan dinkewar tattalin arzikin duniya, lamarin da kasashen duniya ke matukar bukata yanzu. (Ibrahim Yaya)