Wata matar aure mai suna Sadiya Salihu ta garzaya wata kotu a yankin Gwagwalada, inda ta nemi a raba aurenta da mijinta Muhammed Mundi saboda rashin soyayya da kulawa.
Ta shaida wa kotun cewa ta auri Mundi ne a watan Disambar 2022 kamar yadda dokar Musulunci ta tanada.
- 2023: INEC Da ‘Yansanda Sun Nanata Kudirin Samun Sahihin Zabe
- NDLEA Ta Kwace Kwaya Ta N1.5bn Da Cafke Mutum 1,078 Masu Safarar Kwaya A Kano.
”An daura auren nan a Suleja a ranar 17 ga Disamba, 2022, bayan kwana uku da daurin auren na ga wasu sauye-sauye a halayensa.
“A ranar 7 ga watan Janairu ya ce min na shirya kayana domin ya mayar da ni wurin ‘yar uwata a Gwagwalada.
“Na kira mutanena, da suka zo na bi su na dawo Gwagwalada. Lokacin da nake gidan iyayena ya buga waya ya umarce ni da na fito da kayana,” in ji ta.
Ta bukaci kotun da ta raba auren saboda rashin soyayya da kulawa.
Mundi a martaninsa ya ce matarsa ta hana shi yin jima’i da ita.
Alkalin kotun, Malam Abdullahi Abdulkarim, ya shawarci ma’auratan da su sasanta kansu.
Ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 14 ga watan Fabrairu.