Matasan Sin da Afrika, sun gudanar da wani taro ta kafar bidiyo a jiya, domin tattauna yadda za a lalubo hanyoyin inganta kare mabanbantan halittu yayin da suke fuskantar karuwar barazana daga ayyukan bil adama da matsalolin yanayi.
Gidauniyar kula da gandun daji ta African Wildlife Foundation dake da mazauni a Nairobin Kenya da kuma kungiyar masu rajin kare halittu ta Friends of Nature ne suka shirya taron, wanda ya samu mahalarta 190, tare da tattauna hanyoyin shigar da ‘yan asalin yankunan wajen inganta halittu. (Fa’iza Mustapha)
Gwamnatin Biden Na Bin Hanyar Da Tsohuwar Gwamnati Ta Rage Mata Wajen Gudanar Da Harkokin Dake Da Nasaba Da Kasar Sin
Daga CRI Hausa Gwamnatin Biden ta cika wata guda da...