Connect with us

NISHADI

Matasan Zamani                                                                              

Published

on

Gabatarwa Game Da Shafin Matasan Zamani

 

Tare da Sallama Jama’a Assalamu Alaikum! Sunana Ruƙayyat Sadauki, ‘ƴar Jarida mai nazari da bincike gami da sharhi a kan rayuwar matasa ta fuskar nasarori da kuma ƙalubalen da ke haifar wa matasa koma bayan rayuwa a fannoni daban-daban da sauran al’amuran yau da kullum na rayuwar al’umma.

A wannan rana Ina mai farin cikin gabatar muku da wani sabon shiri na musamman mai taken: (MATASAN ZAMANI) wanda zan riƙa gabatarwa a kowacce ranar Juma’a a cikin shafi na musamman da aka warewa shirin a cikin shahararriyar Jaridar nan (Leadership Hausa) wacce ke fitowa a kowacce ranar Juma’a a duk mako.

Shafin (MATASAN ZAMANI) shiri ne na musamman wanda aka tsara shi akan manufar duba ƙalubale da matsalolin rayuwar matasa ta fuskar tattalin arziƙi da sashen ilimi da fannin siyasa da sha’anin soyayya da matsalar auren dole da sauran harkokin zamantakewar rayuwa kamar matsalolin yawan mutuwar aure da rigingimu da shaye-shaye da gurɓacewar tarbiyya a tsakanin matasa maza da mata a gida da makarantu.

A cikin shirin za mu fito da dukkan ƙalubale da matsaloli ɗaya bayan ɗaya sannu a hankali, mu kuma yi sharhi da fashin baƙi akai. Tare kuma da yin bayani mai gamsarwa akan hanyoyin da za abi a magance matsalolin domin samun nasarar cigaba mai ɗorewa a yau da kuma rayuwa tagaba.

Shirin (MATASAN ZAMANI) bai kuma tsaya a iya nan ba, domin kuwa shiri ne wanda zai riƙa gabatar da kyawawan ɗabi’u da halaye da tarbiyya da cigaban rayuwar matasa ta fannoni daban-daban. Haɗe da sharhi da fashin baƙi domin ƙara zaburar da matasa muhimmancin cigaba da riƙe waɗannan kyawawan halaye da matakan cimma nasararsu a rayuwa.

 

Daɗi da ƙari, shirin (MATASAN ZAMANI) shiri ne da zai ba wa masu karatu damar aikowa da tambayoyinsu kan duk abin da ya shige musu duhu ko kuma su aikowa da duk wata matsala da su ke buƙatar a tattauna akanta domin samar da mafita. Zuwa gaba za mu ba da adireshen (Email) da lambobin waya waɗanda za a aike mana da tambayoyi ko neman wani ƙarin haske, mu kuma za mu ba da amsa a rubuce gwargwadon iko.

 

Kamar yadda aka sani, matasa maza da mata su na fuskantar tarin matsaloli ta fannoni daban-daban na rayuwa a wannan zamani waɗanda su ke buƙatar a riƙa tattaunawa da wayar da akan al’umma akansu tare kuma da ƙarawa juna sani domin ganin an gudu tare an kuma tsira tare.

Haka zalika, matasa su ne ƙashin bayan al’umma a duk duniya, idan matasa su ka gyaru su ka hau kan kykkyawar hanya to al’umma ta samu hanyar samun nasarar cigaba. Idan ko matasa su ka kaucewa hanya su ka samu koma bayan rayuwa babu shakka al’umma ce gabaɗaya ta samu koma baya. Dan haka akwai buƙatar mu wayar da kan ƴan uwa matasa maza da mata mu kuma zaburar da su domin samun kykkyawar al’umma mai kykkyawar makoma a yau da gobe.

(MATASAN ZAMANI) shiri ne na matasa domin cigaban matasa, ina fatan matasa da ma sauran al’umma za su yi lale marhabin da wannan shiri wanda ni Ruƙayyat Sadauki zan riƙa shiryawa ina gabatarwa a kowacce ranar Juma’a a shafin (Jaridar LEADERSHI A Yau Juma’a).

Na Gode!
Advertisement

labarai