Wata kotun shari’ar Muslunci da ke zamanta a unguwar PRP a jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Abubakar Ayuba, mai shekaru 20 a duniya da ta samu da laifin yi wa wani Salisu Usaini mummunan rauni a hannu, har ta kai ga hannun ya rube aka yanke shi a asibiti, hukuncin biyan diyyar miliyan 52.
Laifin, a cewar alkalin kotun, Nura Yusuf Ahmad, ya sabawa sashe na 159 na kundin dokar laifuka (Penal Code) ta jihar Kano.
- Babu Wata Shawara Da DSS Ta Aike Wa Buhari Kan Takarar Musulmi Da Musulmi – Fadar Shugaban Kasa
- Rufe Iyakoki Ya Yi Amfani Saboda Mutane Na Cin Shinkafar Gida Yanzu – Buhari
Shi ya sa alkali Ahmad ya yanke wa mai laifin hukuncin daurin watanni shida a gidan yari da kuma biyan diyyar Naira Miliyan 52 da dubu 970 a cikin shekaru ga mai karar.
Alkalin ya kuma umarci wanda a ke karar da ya biya Naira dubu 650 kudin magani ga wanda ya shigar da kara ya yi tun daga farkon jin raunin har zuwa warkewarsa.
Tun da fari dai, a ranar 20 ga watan Maris, 2022 aka zargi Abubakar da daukar wata sharbebiyar wuka ya kuma kaftawa matashi Salisu Usaini a hannunsa na dama, kuma a dalilin wannan aika-aikar ne ya janyo likitoci suka tabbatar da cewar babu shakka sai dai a guntule hannun, saboda tuni hannun ya rube.
Koda likitoci suka cire hannun matashin, sai fa hannu ya ci gaba da rubewa har sai da hakan ya sanya aka sake yi masa aiki, daga karshe kuma sai da aka guntile hannun gaba daya tun daga allon kafadarsa.
Da aka kai mai laifin kotu, mai gabatar da kara, Aliyu Zainul Abideen ne ya karanta wa matashin tuhumar da aike yi masa, tun kuma a wancan lokaci Abubakar ya amsa wannan zargi da a ke yi masa.
Hakan ne ya sanya kotun ta umarci jami’an gidan gyaran hali da su ajiye shi har sai anga yanayin halin da mara lafiyar yake ciki.