Wani matashi dan shekara 20, mai suna Mohammed Sani da ake zargin ya kware wajen sace-sacen na’urorin sanyaya dakuna wato AC a kotuna jihar, ya fada a komar rundunar ‘yansandan Jihar Kaduna.
A yayin da kakakin rundunar ‘yansandan jihar ASP Mansur Hassan ya bajen kolin Sani a gaban ‘yan jairida, Sani ya shedawa ‘yan jaridar cewa, ya kware wajen satar na’urorin a kutuna da kuma na wasu ofis-ofis na gwamnatin jihar.
- EFCC Za Ta Binciki Yadda Kudaden Kananan Hukumomi Ke Sulalewa
- Sin Ta Shirya Daukar Baje Kolin CIIE A Matsayin Wata Dama Ta Gabatar Da Damarmakin Babbar Kasuwarta Ga Duniya
Yaron ya yi ikirarin cewa, wani uban gidansa ne mai suna Isma’il, ke tura shi yin satar ta hanyar bashi wata takarda da ke nuna cewa, wasu mahukunta ne a kotunan ko kuma a ma’aikatun gwamnatin jihar, suka bayar da umarnin a cire na’urorin domin a yi masu gyara.
A cewarsa, shi ne ya sace na’urar sanyaya kotun Majistari da ke a Unguwar Barnawa, inda ya kara da cewa, shi ne, ya sace wata na’urar sanyaya kotun da ke kan titin Ibrahin Taiwo, ya kuma je wata kotu ta shida da nufin sace wata na’urar kotun, amma ba a bashi damar dauka ba
Sannan ya je majalisar dokokin jihar, inda a nan ma, ya saci wata na’urar.
Bugu da kari, ya kuma shiga kotu ta shida da nufin sace wata, amma wasu masu aiki a kotun, suka ce sai na kawo musu takardar izninin kwacewa da dauka.
Ya ce, bayan da na nuna masu masu takardar sai ma’aikatan suka duba takardar, suka ce min ta bogi ce, wanda hakan ya sanya ba su bani damar kwance na’urar ba, ni kuma ban da wata masaniyar cewar ta bogi ce.
“Ban samu nasarar dauka a nan ba, na kira Ismai’ila a waya na shaida masa, sai ya umarce ni cewa, in wuce zuwa kotun Ibrahim Taiwao in kwanto wasu na’urorin, in ji shi.
A cewarsa, asiransa ya tuno ne, bayan da ya samu nasarar kwance na’urorin ya loda su a cikin wani Keke Napape da ya dauko haya, inda wasu ‘yan sanda a kan hanya suka tare Keken, suka kama kayan suka ce sai na kira wanda ya turo ni in dauki kayan.
Ya ce, “ ‘Yan sandan sun tafi da ni, suka rufe ni a caji ofis, suka ce, in kira wanda ya turo ni, na kira wayarsa na sheda masu cewa, an kama ni, sai ya kashe wayarsa, ni kuma ban san inda zan gan shi ba, laifi dai, na aikata, ina neman a yi min afuwa.
Da yake yi wa manema labarai bayani kan batun, ASP Mansur ya ce, matashin yana zuwa yin satar ce da yaudara, inda ya kara da cewa, kafin ya je yin satar, sai bayan ya gama samun sirrin yadda wajen yake.
Ya ce, jami’an ‘yan sandan rundunar sun kuma kwato kayan da yaron ya sace.