A ranar Juma’a majalisar masarautar Bichi ta gudanar da addu’o’i na musamman don neman taimakon Allah a kan matsalar tsaro da ake fuskanta a sassan kasarnan.
Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, ya jagoranci zaman addu’o’in a babban masallacin Juma’a na Bichi.
- Gwamnatin Kano Ta Karawa Dalibanta Kashi 50 Na Tallafin Karatu
- Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano Ta Ceto Mutum 79 A Watan Yuli
Manyan Malamai da Limamai daga kananan hukumomi 9 na masarautar a karkashin jagorancin babban limamin Bichi, Malam Khalifa Lawan Abubakar, ne suka gabatar da addu’o’in.
Malaman sun karanta Al-kur’ani mai girma da niyyar Allah ya kawo mana karshen matsalolin tsaron da kasar nan ke fuskanta.
A jawabinsa bayan kammala addu’o’in, shugaban karamar hukumar Bichi, Farfesa Yusuf Muhammad, ya gode wa masarautar a kan yadda ta shirya adu’o’in yana mai cewa, hakan ya yi daidai musamman ganin yadda kasar ke fuskantar karin matsalolin tsaro a ‘yan kwanakin nan.
Ya kuma nemi al’uma da su gudanar da irin wannan adu’o’in a wuraren zamansu.