Rashin Dawowar Maigida Da Wuri
Assalamu alaikum masu karatu barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon a shafin Uwargida Sarautar mata. A yau shafin na mu zai zo muku da abubuwan da ke kawo matsala a gidan aure. Masu hikima kan ce “idan an san matsala, to an samu rabin maganinta”. Don haka ya kamata mu fahimci asalin matsalolin da ke addabar mu a gidajen aure domin ya ba mu damar sanin ta inda za mu fara magancewa.
Matsalar Farko
Rashin Dawowar Maigida Da Wuri: Wannan matsala ce da na san tana matukar ci wa mata da yawa tuwo a kwarya. Watakila mijinki ma’aikaci ne, ya fita tun safe bai dawo da rana ba, don haka uwargida za ta zaku ta ga maigida ya dawo kafin Magriba. Amma kuma wasu sai bayan Sallar Isha’i suke dawowa. Uwargida ta caba ado tana ta jira har bacci ya fara neman rinjayar ta. Irin wannan matsala ce gaskiya babba a cikin zaman aure. Domin magancewa, yana da kyau uwargida ki fara duba wadannan abubuwan, kina yi ko dai kin rungume hannu ne kina ta cika kina batsewa ke kadai?
Shin yaya yake fita daga gidanki, kina kokarin kin saka shi a cikin farin ciki da annashuwa kafin ya fita ko dai da fada kuke rabuwa? Ya kama uwargida kisan cewa kafin maigida ya fita kin yi kokarin yadda za ki sa shi ya fita yana farin ciki, kin yi abinci ya ci, kin shirya shi, wato ina nufin za ki iya yi wa mijinki wanka ki shafa masa mai kin sa masa kaya ki hula ki sa idan ba mai amfani da suit bane, idan mai sa suit ne ki tabbatar kin iya yadda ake kayan suit kin iya daura belt ki sa masa safa da takalmi ya fito tsaf ki kamo hannunsa ki raka shi idan mai mota ne ki kai shi har mota ki bude masa ya shiga ki masa fatan alkhairi tare da addu’ar samun nasara ki gani kafin a tashi a wajen aiki zai rika matsuwa a yi a tashi saboda ya koma gida.
 Shin idan ya fita wane irin sako kike aika masa? Ko dai ke ‘yar ba ruwana ce da me cewa idan aka biye wa namiji babu abin da za a kulla a rayuwa? Kin yi shiru, kin kyale maigida ko tunawa da shi ba kya yi ballantana ki aika masa da dadaddan sakonni da zai sa ya ji shi kansa ya zaku ya dawo gida kuma abin Allah ya kiyaye, wata tana can tana tunani da zakulo sabbin dabarun sace zuciyarsa ke kuma kin zauna shiru, an ya kuwa a haka yaki ba zai ciki ba? Yana da kyau ki rika aika masa da sakonni da za su nuna masa cewa shi ne fa a gaban ki kuma tabbas yana da wadda ta damu da shi. Ba kiran waya za ki rika yi ba a kai a kai, a’a, watakila wani aikinsa ba ya son haka, amma sako, duk lokacin da ya samu sarari zai duba.
 Abu na gaba shi ne, yaya kike karbarsa idan ya dawo gida kuma a wane hali yake samunki, ya yanayin gidanki yake, ya makwancinsa yake? Na tabbatar da cewa duk wadannan tambayoyin kin san amsarsu, abin da ya rage shi ne ki kimtsa masa kanki, kar ki tarbe shi da kayan da kika yi girki a jikinki, ki gyara gidanki, ki kimtsa yara tsaf sannan da ya shiga daki ya tarar da abin da zai kara kwantar masa da hankali cewa lallai ya dawo gida, wato ki iya shimfada kado wani namijin shimfida kado kadai tana kwantar masa da hankali yaji yana san wannan mai shimfadar a kusa da shi amma da yawa wasu matan basu iya shimfadar gado ba sai ki ga can zanin gado ya cikorkode can ya shamide, wata kuma daga ranar da ta sake zanin gado ba za ta sake shimfada ba sai randa ya yi datti za ta canja wani, lailaya shimfadar gado tanajan hankalin namiji sosai ya ji zai huta ba zai so ya tashi ba, wata kuwa ko kayan da ya je akan gadon ba za ta dauke ba har sai sanda ya dauke abin sa saboda ba ta damu da gyaran gadon ba.