Damuwar da ke tsakanin al’ummar Nijeriya game da matsalar karancin abinci da ake fama da ita ta yi tsananin gaske. Ana ta cece-kuce kan batun karancin abinci a kasar; abubuwan da suka faru na baya-bayan nan kawai sun isa su tashi hankulan jama’a. Kasancewar har yanzu ana fama da barnar ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga a jihohi irin su Benuwe, Neja, Filato, Kaduna da Zamfara, akwai matukar fargabar cewa al’ummar wadannan jihohi ba za su iya ba da gudummawa ga samar da wadataccen abinci a kasar nan ba.
Mutane na ta korafi har ma an fara tunanin yin gagarumar zanga-zanga a karshen wannan wata, kamar yadda ake ta yekuwa a shafukan sada zumunta.
- CAF 2025: Nijeriya Ta Fito A Rukuni Mai Zafi
- Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (3)
Rikice-rikice da rashin tsaro, hauhawar farashin kayayyaki, da matsalar sauyin yanayi na ci gaba da kawo cikas ga samar da abinci a Nijeriya na tsawon wani lokaci zuwa yanzu. Kimanin mutane miliyan 26.5 a fadin kasar ana hasashen za su fuskanci matsananciyar yunwa a cikin watannin Yuni zuwa Agusta na 2024, karin da aka samu mai ban mamaki idan aka kwatanta da mutane miliyan 18.6 da ke fama da karancin abincin a karshen shekarar 2023.
Akwai rahotannin da ke nuna cewa karuwar satar mutane don neman kudin fansa daga Disamba zuwa Fabrairu ta haifar da fargaba da kuma barazana ga ayyukan samar da kudin shiga. Ya zuwa watan Fabrairu, talakawa magidanta sun yi wa rumbunan hatsinsu karkaf, wanda hakan ya haifar da dogaro da sayen abinci a kasuwa. Baya ga wannan, har ila yau, rashin bunkasar tattalin arziki ya kara tagayyara sayayyar kayan masarufi da iyalai ke yi.
Wannan jarida ta damu matuka da tasirin wadannan abubuwa ga harkar manoma. Ana tilasta wa ’yan Nijeriya masu aiki tukuru wajen neman halaliyarsu, barin gonakinsu, ana lalata musu amfanin gonakinsu a wuraren da suka samu damar noma. Hakan na nufin ana samun raguwar kayan abinci a yankunan da abin ya shafa, kuma jama’a sun rasa abin da za su ci balle a yi zancen sayarwa a samu na rufin asiri. Misali a Jihar Neja, ‘yan ta’adda sun kwace filayen noma kuma suna ci gaba da amfani da su. Wannan lamari ne da ke nuni da yadda lamarin ya tabarbare.
Hare-haren ‘yan bindiga na baya-bayan nan da aka ruwaito a wasu kauyuka hudu na Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja, sun raba mutane 600 da muhallansu duk da cewa suna amfani da mutanen kauyukan ta hanyar tilasta musu aiki a gonakin da suka kwace ba tare da kuma suna biyan su ladan kwadagonsu ba. Yankunan da abin ya shafa sun hada da kauyukan Lanta, Tunga, Dnakau, da Juweedna na Erena a Karamar Hukumar Shiroro. Mazauna kauyen sun yi watsi da gonakinsu.
Har ila yau, rikicin yankin Arewa maso Gabas ya yi sanadin raba mutane miliyan 2.2 da matsugunansu, sannan wasu miliyan 4.4 na fuskantar karancin abinci a jihohin Borno, Adamawa da Yobe. Miliyan uku daga cikinsu suna jihar Borno ne, da ta zama cibiyar tashe-tashen hankula a wannan yankin. Nijeriya kan yi fama da fari da ambaliyar ruwa a wasu lokuta. Wadannan ma sun kara tagayyara noma da kuma kara wa jama’a rauni musamman a yankunan karkara.
A cewar Hukumar Abinci ta Duniya (WFP), ayyukan ‘yan ta’adda da masu tayar da kayar baya sun kara matsin lamba ga yanayin albarkatun kasa, da rashin tsaro, da kawo cikas ga ci gaba, da kuma kara tsananta rashin abinci da abinci mai gina jiki na mata da yara masu rauni. WFP ta mayar da hankali wajen ganin tana kai wa ga marasa galihu miliyan 1.1 duk wata a arewacin Nijeriya. Wadanda ke samun taimako sun hada da mutanen da suka rasa matsugunansu da ke zaune a sansanonin ko kuma al’ummomin da suka karbi bakuncinsu, da su kansu talakawan al’ummomin da ke karbar baduncin, da kuma mutanen da ke komawa gida bayan shafe watanni suna gudun hijira.
Hijira daga karkara zuwa birni wani babban al’amari ne da ke shafar noma da kuma, samun wadatar abinci a yankunan karkara. Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), a kwanan nan ta ruwaito cewa hauhawar farashin kayan abinci a watan Mayu ya karu zuwa kashi 40.66 bisa dari, karin kashi 15.84 da aka samu ya nausa daga kashi 24.82 da aka samu a watan Mayun 2023.
Mummunan halin da ake ciki ya sa muke kira ga gwamnati da ta dauki tsauraran matakai don magance matsalar rashin tsaro a Arewa. Hakazalika, dole ne gwamnati ta fahimci cewa samar da abinci wani muhimmin hakki ne na Dan’adam, kuma alhakin gwamnati ne ta tabbatar da cewa ‘yan kasar sun samu isasshen abinci don ciyar da kansu da iyalansu. Hakan na nufin dole ne gwamnati ta dauki kwakkwaran mataki na magance matsalolin rashin tsaro da kuma samar da isasshiyar kariya ga manoma da amfanin gonakinsu.
Shawarar da gwamnati ta yanke ta cire haraji ga shinkafa, wake da alkama da za a shigo da su aba ce da ta dace. Amma ya kamata a yi cikakkiyar aiwatar da ita.
Haka kuma gwamnati za ta iya daukar matakan karfafa gwiwar zuba jari a harkar noma da bayar da tallafi ga kananan manoma. Wannan na iya hadawa da ba da damar samun lamuni, horo, da taimako da fasahar zamani. Haka kuma gwamnati na iya yin aiki tare da abokan huldar kasashen duniya don samar da kudade da taimakon aiki da fasahar zamani don tallafa wa bunkasa noma a Nijeriya.
Baya ga matakai da abubuwan da gwamnati za ta yi, kungiyoyin fararen hula da kuma kamfanoni masu zaman kansu na iya taimakawa wajen magance matsalar karancin abinci a Nijeriya. Wadannan kungiyoyi za su iya yin aiki tare da manoma don ba da tallafi daidai gwargwadon da za su iya da kuma bayar da shawarwari ga manufofi da shirye-shiryen da ke inganta samar da wadatar abinci.
Matsalar karancin abinci a Nijeriya, ko shakka babu, lamari ne da ke bukatar kulawar gaggawa daga dukkan masu ruwa da tsaki. Dole ne gwamnati ta mike haikan ta magance matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a Arewa da ma sauran sassan kasar nan, tare da inganta harkokin noma, da tallafa wa kananan manoma.
Su ma kungiyoyin fararen hula da masu zaman kansu dole ne su taka rawa wajen magance wannan matsala. Bisa hadin gwiwa, kasar za ta iya kawar da matsalar karancin abinci da ke kunno kai tare da tabbatar da cewa dukkan ‘yan Nijeriya sun samu isasshen abinci da za su iya ciyar da kansu da iyalansu.