Nasir S Gwangwazo" />

Mayar Da Matasa Saniyar Ware A Fannin Mulki

A Nijeriya, tarihi ya na cigaba da maimaita kansa, inda a ke mayar da matasan kasar saniyar ware a duk lokacin da a ka zo matakin rabar da mukaman gwamnati, inda hakan ya fito a fili kan mukaman da a ka rabar kuma a ka ajiye su matasan a gefe guda. Hakan dai ya samu asali ne tun a Jamhuriyya ta Biyu, inda har yanzu a ke cigaba da yin hakan har zuwa yau a kasar. Lamarin ya fi kyau a lokacin a mulkin mallaka da kuma lokacin da a ka samu mulkin kai a kasar, inda matasa daga masu shekaru 20 zuwa 30 a ke damawa da su a fannin mulki. Hakan ya janyo jefa rayuwar matasan kasar a cikin halin tsaka-mai-wuya, inda wasu su ka gwammace su rungumi hanyar yin maula ko zama ’yan barandan siyasa a matsayin hanyoyin da za su taimaka wa kawunansu. Mafi yawancin matasan rayuwar matasan Jamhuriyya ta Biyu ta sha bamban da rayuwar matasan yau, ganin cewar, rayuwar matasan na yau ba su da wata kwarewa ko isasshen ilimin boko. Wannnan shi ne ra’ayin wannan jaridar, saboda ganin cewar, an mayar da matasan kasar saniyar ware a bangatren da ya shafi sanya su a cikin harkar gudanar da mulki. Tun daga fannin shari’a da bangaren zantarwa, dukkan mukaman da a ke rabarwa, sai ’yan mowa ne, amma ’yan bora an bar su a gefe, ba a damawa da su. Alal misali; tantance sunayen wadanda za a bai wa mukaman ministoci da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabatarwa da Majalisar Dattawa, don a tantance su, a kuma tabbatar da su, hakan ya nuna a zahiri matasan kasar a na kara ture su a gefe, inda dattawa su ke cigaba da ci da gumin matasan kasar ta fannin samun mukaman gwamnati. Duk dokar da ta bai wa matasa damar rike madafun iko a kasar da a ke kira a turance ‘Not-Too-YoungTo-Run’ a duk wadannan ranakun da kuma zuwa lokacin da a ka yi zaben gama-gari na 2019 a na ta gudanar da ayyukan siyasa, inda manyan jam’iyyun siyasun kasar, APC da kuma PDP, su ka gudanar da manyan gangami a kan lamarin da ya shafi mata da matasa. An yi wa matasan alkawura, inda su ka yi amanna cewar lokacinsu ne ya zo, inda kuma su ka bazama wajen nema wa ’yan takara masu goya mu su ,baya don su lashe zabubbuka daban-daban. Idan za mu iya tunawa, a lokacin Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugabannin ’yan kungiyar ‘Not- Too- Young –To- Run’ a fadar shugaban kasa da ke garin Abuja, ya shaida mu su dalilin da ya sanya ya sa hannu a kan kudurin  na ‘Not- Too- Young –To- To- Run’ har ya zamo doka, inda ya roke su da su ba shi goyon baya, don yin tazarce a karo na biyu na wa’adin mulkinsa. Ya kuma yi mu su alkawarin nada matasa da mata a mukamai idan har ya lashe zaben, inda a saboda hakan ne tawagar matasa ’yan APC su ka gabatar da takarda dauke da sunayen matasa 100 da su ke bukatar Buhari ya nada su a mukaman ministoci da suran mukamai, don ya yi duba a kai. Takarda ce da matasan su ka tsara ta yadda ya dace, amma sai dai ba ta yi wani amfani ba. Amma abin takaici da kuma damuwa shi ne, babu mai shekara 40 zuwa 44 da a ka nada a mukamin minista, inda hakan ya nuna a zahiri matasan ba su da wani wakilci a gwamnatin ta Buhari. Har su ma matan da a ka lasa wa zuma a baki an ajiye su a gafe, inda kawai daga daya zuwa shida a wa’adin mulkin Buhari zuwa bakwai a ka  nada a mukamai, mu na da yakinin har yanzu lamarin ba ta canja zani ba. Tunda ya ke cewa, Buhari mai sauraron koke ne, mu na kira a gare shi da ya yi dubi a kan lamarin, saboda ganin yadda a ke mayar da matasan da kuma mata saniyar ware. Babu wata tantama cewa, matasan kasar su na da hazaka kuma za su iya rike dukkan irin matakan gwamnati da a ka nada su na mukami a kasar, ya kuma kamata Buhari ya fara wanzar da dokar ta ‘Not-Too- Young-To- Run’, inda rashin yin hakan zai iya janyo sabawa dokar, musamman ganin cewa, matasan kasar su ne su ka fi sauran al’umma yawa a kasar. Tabbasa wadanda a ka nada mukaman na ministocin babu cikakkun matasa sai kalilan kuma ba su da wani wakilci. Har nakasassu su ma an bar su a baya. Ya kamata APC mai muliki da kuma maganar mataki na gaba, ta sani cewa, an yi wa matasa alkawuran samun mukamai, amma daga baya a ka share su, sabanin yadda a wasu kasashen duniya a ke damawa da matasa takwarorinsu. A saboda haka, mu na rokon Buhari da ya yi dubi a kan wadanda zai nada a wasu mukaman nan gaba, musamman don kada a bar matasa a baya.

 

Exit mobile version