Cacar baki ta kaure a tsakanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso da jam’iyyar PDP.
Zazzafar mahawarar dai ta fara ne tun lokacin da Kwankwaso ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta mutu a siyasance.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Matafiya A Babbar Hanyar Gusau-Funtua
- Kotu Ta Bada Belin Masu Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa Kan Naira Milyan 10 Kowanensu
Da yake magana a ranar Asabar a yayin bude wani ofishin jam’iyyar NNPP da aka yi wa gyara a Jihar Katsina, Kwankwaso ya ce shi da mabiyansa sun bar PDP ne saboda ta mutu.
“Ina so in tunatar da ku cewa PDP ta mutu saboda mun bar jam’iyyar. Tun da sun fita daga layi sai muka yanke shawarar ficewa,” in ji shi.
Kwankwaso ya kuma ce shi ne zai lashe zaben shugaban kasa a 2027, inda ya ce jam’iyyar NNPP a shirye take ta karbi ragamar shugabancin kasar da sauran jihohi.
Tsohon gwamnan Jihar Kano ya ce bai kamata a yaudari ‘yan Nijeriya da kyauta ko kudi ba a lokacin zabe mai zuwa.
Da take mayar da martini, jam’iyyar PDP ta bayyana cewa Kwankwaso bai da alkibla a siyasar Nijeriya, wanda hakan ta sa ya gaza ya kuma rasa kimansa.
Jam’iyyar PDP ta mayar da martanin ne a cikin wata sanarwa ta hannun sakataren yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba, ta soki Kwankwaso da nuna son kai da son zuciya wanda ke nuni da cewa shi ba shugaba ne nagari ba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Martanin da muka mayar dangane da kalaman da Sanata Rabi’u Kwankwaso shi ne, ba shi da wani tasiri a siyasar Nijeriya a yau idan aka yi la’akari da yadda yake fafutukar shugabancin jam’iyyar mai suna NNPP wadda ita ma ke fafutukar ganin ta mallaki jiha daya kawai.
“Abun takaicin ne a cewa dan siyasar da ya gaza kuma mara tasiri da ke da jiha daya zai yi ikirarin cewa jam’iyyar da ke da gwamnoni 13, da sanatoci da dama da ‘yan majalisar wakilai masu yawa da a dukkan rassan kasar nan.
“Abin da ya fi tayar da hankali shi ne, yadda Sanata Kwankwaso ya nuna tsananin son kai da son zuciya, wanda hakan ke nuna cewa shi ba shugaba ba ne.”
Jam’iyyar PDP ta bayyana Kwankwaso a matsayin dan siyasar mara alkibla da wanda ya samu nasarorinsa ta hanyar tsarin jam’iyyar PDP.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Abin takaici ne a wannan lokaci da jam’iyyar PDP da ‘yan Nijeriya masu kishin kasa ke tofa albarkacin bakinsu dangane da tsananin wahalhalun da kasar nan ke fuskanta sakamakon manufofin gwamnatin APC na kin jinin jama’a, a wannan lokacin ‘yan Nijeriya ciki har da gidan Sanata Kwankwaso na Jihar Kano na fama da yunwa.
“A daidai lokacin da ‘yan Nijeriya sama da miliyan 150 suka tsunduma cikin bakin talauci, a kullum miliyoyin ‘yan Nijeriya ke asarar hanyoyin samun abinci a lokacin da darajar naira ta fadi zuwa fiye da naira 1,600 kan dala daya, sannan an samu kashi 34 na hauhawar farashin man fetur wanda ya kai lita daya naira 1,200 a sannan kasar nan sakamakon munannan manufofin APC. Burin Sanata Kwankwaso shi ne son zama shugaban kasa ba tare da nuna damuwa kan halin da kasar nan ke ciki ba. Wannan babban abin takaici ne matuka.
“Don haka jam’iyyar PDP ba za ta tsaya cacar baki da shi ba kan irin wannan nuna son kai da rashin sanin ya kamata. Ko ta wace fuska, duk nasarar da Kwankwaso ya samu a siyasance, ya samu ne ta sanadiyyar PDP.”
Wannan dambarwa dai ta sake jefa shakku a kan yiwuwar kawancen da ake tunanin zai iya kulluwa a tsakanin Atiku da Kwankwaso da kuma Obi domin yi wa Shugaban Kasa Tinubu taron dangi a shekarar 2027.
Kana tambayar da ake dakon amsarta har yanzu ita ce, me ya haddasa wannan cacar bakin a tsakanin Kwankwaso da PDP?