Hukumar kula da fitar kaya ta kasa (NEPC), ta nuna damuwarta kan rashin samun riba mai yawa daga hada-hadar kasuwancin Alabsar, duk kuwa da cewa; Nijeriya na daya daga cikin kasashen da ke gaba a fadin Afirka wajen nomanta.  Â
Duk da cewa, a duk shekara ana noman Albasa kimanin tan miliyan biyu, amma adadin Albasar da ake nomawa a kasar ya yi matukar yin kasa, wanda hakan na faruwa ne sakamakon amfani da gundarin Albasar wajen yin wasu nau’ikan abubuwa daban-daban a wannan kasa.
Hai ila yau, masu ruwa da tsaki ne suka bayyana haka; a wani taron tattauwa a kan dabarun bunkasa nomanta da aka gudanar a Jihar Gombe.
Babbar Darakta ta hukumar NEPC, Nonye Ayeni a jawabinta a wajen taron, ta bayyana kalubalen da ake fuskanta a bangaren hada-hadar kasuwancin Albasar a Nijeriya.
Kazalika, ta sanar da haka ne; ta hanyar wakilinta a wajen taron Mustapha Umar Faruk, inda ya bayyana cewa; an jawo jihohi kamar su Gombe, Sakkwato, Kebbi, Zamfara, Katsina, Kano, Kaduna, Jigawa, Yobe, Borno, Bauchi, Taraba, Filato da kuma Abuja, a wannan fanni na noman Albasar.
Ta ci gaba da cewa, sai dai har yanzu Nijeriya ta gaza ci gaba da rike matsayinta a faninn hada-hadar kasuwancin na Albasa, musamman sakamakon rashin iya sarrafa ta da kuma yin amfani da dabarun fitar da ita zuwa kasashen ketare.
Nonye ta kara da cewa, saboda rashin kimanta Albsar a kasar nan ne, yasa ake samun raguwar samun ribarta da kuma raguwar saumun kudaden shiga daga fitar da ita da ake yi zuwa kasashen ketare.
A cewarta, wannan dalili ne yasa hukumar ta hanyar wannan shiri ta samu nasarar tattaunawa da masu ruwa da tsaki, domin bunkasa dabarun fitar da ita zuwa kasashen ketare.
A cewar tata, hakan zai bai wa Nijeriya damar aiwatar da gasa a kasuwannin duniya, musamman a wannan bangare na hada-hadar kasuwancin Albasa, a tsakaninta da sauran kasashen duniya.
Nasiru Aliyu, Kwamishina Ma’aikatar Kasuwanci da Zuba Jari; yaba wa hukumar ya yi a kan shirya taron. Inda ya sanar da cewa, taron ya zo a kan gaba duba da karuwar wayar da kan manoman Albasar.
Kwamishinan, wanda Babban Sakatare a Ma’aikatar; Babayo Hassan Abubakar ya wakilta a wajen taron, ya bukaci manomanta su kara yin kokari wajen noma ta; ba tare da dogaro ga gwamnati ba.
Shi kuwa, Shugaban Kungiyar Manoman Albasa na Shiyyar Arewa Maso Gabas; Alhaji Sani Pantami; yaba wa hukumar ya yi a kan ilimantar da manoman da sauran masu ruwa da tsaki da ta yi, musamman a kan muhimmancin kasuwancin Albasa na kasa da kasa.
Ya kuma yi waiwaye a kan kalubalen da manoman suke fuskanta a baya, da suka hada da yin asara sakamakon rashin kwarewar da suke da ita na fitar da Albasar zuwa kasashen na ketare, domin sayar da ita.
Sai dai, ya yi nuni da cewa; bisa ilimin da suka samu ta hanyar shirin ya ce, yana da yakinin cewa; akasarin manoman a halin yanzu zai ba su kwarin gwiwar sanin dabarun noman Albasar, musamman ta hanyar samun ingantaccen Irin nomanta.