Cikin manufofin raya kasa na Najeriya da na sauran kasashen dake nahiyar Afirka, duk an ambato cewa za a yi kokarin raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba. Sai dai, a wani lokaci a kan ga yadda mutane suke shakku game da batun, suna tambaya cewa: Me ya sa muke ware kudi ga bangaren kare muhalli, duk da cewa ana matukar bukatar raya tattalin arziki cikin gaggawa a Afirka?
Tun da akwai tambaya, to, ya kamata mu nemi amsa, da cimma matsaya, maimakon kai-komo tsakanin mabambantan manufofi. A wannan wata da muke ciki, aka cika shekaru 10 da kasashen duniya suka sa hannu kan yarjejeniyar Paris ta tinkarar sauyawar yanayin duniya. A cikin shekarun 10 da suka wuce, matakan da mutanen duniya suka dauka a hadin gwiwarsu sun rage adadin hauhawar zafin yanayin da ake sa ran samu daga digiri 4 zuwa digiri 2.8, bisa ma’aunin Celcius, duk da cewa bai kai digiri 1.5 da ake son samu ba. Kana wani babban dalilin da ya hana dan Adam samun biyan bukata a wannan karo, shi ne wasu kasashe suna amai suna lashewa a fannin aiwatar da matakan kare muhalli. Misali, kasar Amurka ta taba janye jikinta daga yarjejeniyar Paris har sau biyu, kuma har yanzu ba ta amince da yarjejeniyar ba, ko da yake kasar ce ke fitar da mafi yawan iska mai dumama yanayi a tarihin dan Adam.
Sai dai me ya sa ake bukatar raya tattalin arziki tare da kare muhalli?
Dalili na farko shi ne, babu sabani a tsakanin batutuwan 2, wato kare muhalli da bunkasa tattalin arziki.
Wani rahoton da dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya ya fitar a kwanan baya, ya ce darajar tattalin arziki mai alaka da batun kare muhalli a duk duniya ta riga ta zarce dalar Amurka triliyan 5 a shekarar 2024, adadin da zai haura triliyan 7 a shekarar 2030. Wato wannan bangare yana cikin fannoni mafi samun karuwar daraja a duk duniya.
Sa’an nan idan mun dauki kasar Sin a matsayin misali, to, za mu ga kasar tana tsayawa kan manufarta ta “Daukar muhalli mai inganci a matsayin damar samun ci gaban tattalin arziki”, inda sana’o’i masu alaka da kare muhalli suka zama muhimmin karfin da ke sa kaimin tattalin arzikin kasar. Kana ana hasashen cewa, darajar bangaren sana’o’in kare muhalli na kasar Sin za ta kai dalar Amurka triliyan 2.12, nan da shekarar 2030.
Kana dalili na biyu da ya sa ake kokarin kare muhalli a kasashen Afirka, shi ne, akwai dimbin albarkatu a yankunansu, wadanda za a iya amfani da su wajen raya tattalin arziki tare da kare muhalli.
Idan mun dauki bangaren makamashi a matsayin misali: Daukacin karfin ruwa a nahiyar Afirka ya kai Megawatts miliyan 115.5, wanda ya ninka karfin tashoshin samar da wutar lantarki ta karfin ruwa da aka gina a Afirka har sau 34. An ce idan an samu damar amfani da karfin ruwa sosai, to, ko kogin Congo shi kadai ma zai iya biyan bukatar daukacin nahiyar Afirka a fannin wutar lantarki a yanzu. Ban da haka, kasashen Afirka suna da cikakken boyayyen karfi a fannin samar da wutar lantarki ta zafin rana, da karfin iska, da sauran makamashi masu tsabta. Bisa hasashen da hukumomin kasa da kasa masu kula da makamashin da ake iya sabuntawa suka yi, ya zuwa shekarar 2030, karfin samar da wutar lantarki ta wannan nau’in makamashi a nahiyar Afirka zai kai Gigawatts 310, adadin da zai kasance kan gaba a duniya.
Sa’an nan, dalili na uku na dacewar manufar kare muhalli ta kasashen Afirka, shi ne, kasashen suna samun cikakken goyon baya daga kasar Sin a wannan fanni.
Dimbin misalai sun shaida cewa, kamfanonin kasar Sin suna taka rawar gani wajen taimakon kasashen Afirka raya tattalin arzikinsu ta wasu dabaru masu kare muhalli. Haka zalika, kasar Sin tana kokarin gabatar da fasahohin zamani na kare muhalli ga kasashen Afirka, karkashin tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa a duniya.
Duk wadannan dalilan da muka ambata sun nuna cewa, aikin raya tattalin arziki tare da kare muhalli a nahiyar Afirka na da makoma mai haske. Don haka, kamata ya yi, a tsaya kan hadin gwiwa tare da abokan hulda don raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta wasu dabaru masu kare muhalli, ta yadda za a iya tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasashen, gami da samar da gudunmowa ga yunkurin tinkarar sauyawar yanayi a duniya. (Bello Wang)














