Connect with us

WASANNI

Messi Ba Ya Jin Dadin Rashin Kokarinsa -MASCHERANO

Published

on

Dan wasan tsakiyar Argentina, Jabier Mascherano ya bayyana cewa shahararren dan wasan kasar, Leonel Messi bayajin dadin rashin kokarinsa a wasanni biyu daya buga kawo yanzu a gasar cin kofin duniya da take gudana a kasar Rasha.
Kasar Argentina ce dai ta karshe a cikin rukunin bayan data buga 1-1 da kasar Iceland a wasan farko kafin kuma tasha kashi a hannun kasar Crotia daci 3-0 matakin dayasa abune mai wahala kasar wadda Messi yake jagoranta ta iya fitowa daga cikin rukunin.
”Messi baiji dadi ba daya zubar da bugun fanareti a wasan Iceland kuma yaji haushi sosai amma kuma haka zai hakura saboda haka sakamakon wasan zai kasance amma kuma yana nan yana shiryawa a wasan yau” in ji Mascherano
Yaci gaba da cewa Messi yana cikin farin ciki sosai sai dai rashin samun nasarar yana damunsa sosai kamar yadda yake damun dukkanin yan wasanmu.
Sannan yace Messi mutum ne kamar kowa kuma yana jin bakin ciki idan har bai samu nasara ba kuma yanason ya gyara kurakuren da akayi a baya har ila yau yana son ya nunawa duniya cewa zai iya dawo da nasarar Argentina.
Kasar Argentina dai tana bukatar dole sai ta samu nasara akan Nijeriya domin samun nasara zuwa mataki na gaba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: