Messi Ya Buga Wasa Na 147 A Argentina

Argentina

Dan wasan kungiyar kwallon  kafa ta Barcelona, Lionel Messi ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Argentina wasa na 147 a karawar da suka doke kasar Paraguay, suka kai daf da na kusa da na karshe a Copa America.

Dan wasan mai shekara 34 a duniya ya yi kan-kan-kan da dan wasa Jabier Mascherano wajen yawan buga wa tawagar ta Argentina wasanni sai dai tuni Mascherano yayi ritaya daga bugawa kasar wasa.

Argentina ce ta ja ragamar rukuni na daya, bayan da Chile ta tashi 1-1 da Uruguay, wadda itama ta kai zagayen gaba kuma wannan gasar dama ce ta karshe da Messi zai lashe kofi a babbar tawagar Argentina da bai samu damar daukar ba.

Dan wasan Barcelona bai taba lashe kofi a babbar kungiyar Argentina ba, illa dai ya daga kofin duniya a tawagar matasa ta ‘yan kasa da shekara 20 a shekarar 2005 kuma gasar Copa America da ake yi a Brazil a bana an tsara yi a Argentina tun farko, amma tsoron yada cutar korona ta sa aka dauke gasar daga kasar.

Messi wanda ya lashe Ballon d’Or shida na taka rawar gani a gasar Copa America ta bana, duk da cutar korona da ke kai tsaiko a wasannin kuma saura wasa hudu suka rage a rukunin farko, inda Paraguay keda maki uku, Uruguay daya ne da ita da Bolibia mara maki ko daya.

Hakan na nufin kowacce tana da damar kai wa zagayen gaba, kamar yadda Argentina da Chile suka yi kuma tuni Brazil mai masaukin baki ta kai karawar daf da na kusa da na karshe a rukuni na biyu.

Exit mobile version