Ɗan wasan Barcelona Lionel Messi ya ci ƙwallo ta 100 a wasannin cin kofin Nahiyar Turai, bayan da Barcelona ta ci Olympiakos 3-1 a gasar Zakarun Turai da aka fafata a ranar Laraba a filin wasa na Nou Camp.
Barcelona ta fara cin ƙwallo a minti na 18 da fara wasan, bayan da Dimitris Nikolaou ya ci gida.
Bayan da aka dawo ne Lionel Messi ya ƙara ta biyu, sannan Lucas Digne ya ƙara ta uku, sai dai ƙungiyar ta kammala karawar da ‘yan wasa 10 a fili bayan da aka bai wa mai tsaron bayansu Piƙue jan kati.
Sai dai kuma ana dab dalokacin tashi daga karawar Olympiakos ta zare ƙwallo ɗaya ta hannun Dimitris Nikolaou, ɗan shekara 27
Da wannan sakamakon Barcelona ta haɗa maki tara sai Juɓ entus da maki shida, sai Sporting da maki uku sannan Olympiokos ta ƙarshe wacce ba ta da maki ko ɗaya a matsayi ta ƙarshe.