Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi ziyarar aiki a kasar Amurka daga ranar 23 zuwa 25 ga watan nan. Bayan ziyarar, memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda har ila yau shi ne ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya yi tsokaci kan wannan ziyara ta shugaba Xi ga manema labarai.
Wang Yi ya ce, shugaba Xi Jinping ya yi wata doguwar tafiya don ziyartar kasar Amurka, ziyarar da ta jawo hankalin duk duniya, wadda ta zama ziyarar aiki da shugaba Xi ya sake yi bayan shekaru 11. Kazalika, Wang Yi ya ce, ziyarar ce ta sa shugabannin kasashen biyu suka cimma nasarar kawo wa juna ziyara cikin rabin shekara, tare da kafa tarihin mu’amalar Sin da Amurka.
Bugu da kari, kafafen yada labarun Sin da na kasashen waje sun mayar da hankali sosai kan ziyarar Xi a wannan karo, inda a ganinsu, ta zama ziyarar tarihi mai cike da babbar ma’ana. Yayin da duniya ke fuskantar tashe-tashen hankula, ziyarar ta kara yayata nasarorin da aka samu a yayin ganawar shugabannin biyu a Beijing, da jagorantar samun karin ci gaba wajen raya kyakkyawar dangantakar Sin da Amurka mai gudana bisa daidaiton manyan tsare-tsare, da shaida cewa, Sin da Amurka suna nuna wa juna goyon-baya da zaman jituwa da kuma samun moriya tare, a wani kokari na samar da alfanu ga kasashen biyu gami da duk duniya baki daya.(Murtala Zhang)














