ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, November 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

MTN Ta Dakatar Da Tsarin Bayar Da Bashin Data Da Kati, Duba Dalili

by Abubakar Sulaiman
7 months ago

Kamfanin sadarwa na MTN Nijeriya ya sanar da dakatar da tsarin bayar da rancen kati da data, wato Xtratime, na ɗan lokaci bayan sabbin ƙa’idoji da Hukumar Kare Gasa da jama’a (FCCPC) ta ƙaddamar. Kamfanin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya aika wa Kasuwar Hannayen Jari ta Nijeriya a ranar Alhamis, yana mai cewa matakin ya zama dole domin bin sabbin dokoki na shekarar 2025.

Xtratime, wanda masu amfani da layukan biya kafin amfani ke yawan amfani da shi, yana bai wa kwastomomi damar aron kati ko data su biya daga baya lokacin da suka sake saka kuɗi. A cikin sanarwar da Sakataren Kamfanin, Uto Ukpanah, ya sanya wa hannu, MTN ta tabbatar da dakatarwar tare da cewa matakin na wucin gadi ne.

Yadda Rashin Biyan Bashi Tsakanin Surukai Ke Shafar Zamantakewar Aure

ADVERTISEMENT

Bai Kamata Gwamnati Ta Ke Ciyo Bashi Bayan Cire Tallafin Man Fetur Ba – Sanusi II

Kamfanin ya bayyana cewa sabis ɗin yanzu ya shiga ƙarƙashin sabbin ƙa’idojin FCCPC da suka shafi ba da rance ta hanyar dijital, waɗanda ke buƙatar sabon lasisi da kuma bin tsauraran Sharuɗɗa. An ce wannan na daga cikin tsarin “Digital, Electronic, Online or Non-Traditional Consumer Lending Regulations, 2025” da ya ƙara faɗaɗa kulawa ga irin waɗannan ayyuka.

LABARAI MASU NASABA

Yawaitar Tashin Gobara A Kasuwannin Kano, Shin ’Yan Kasuwa Na Samun Kulawar Da Ta Dace?

Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Jawo Hankalin Masu Zuba Jari Daga Ƙasashe 120

Duk da dakatarwar, MTN ta tabbatar wa abokan hulɗarta cewa har yanzu ana iya siyan kati da data ta hanyoyi daban-daban ba tare da wata matsala ba. Haka kuma ta rage muhimmancin tasirin matakin a harkar kuɗin shiga, tana mai cewa ba sa tsammanin zai yi wani babban tasiri ga kuɗaɗen kamfanin.

Sabbin ƙa’idojin FCCPC na shekarar 2025 sun ƙara tsaurara sa ido kan kamfanonin da ke bayar da rance ta hanyar dijital a Nijeriya, inda ake buƙatar su yi rijista da samun amincewa kafin ci gaba da aiki. An kafa wa kamfanoni wa’adin daidaitawa da dokokin zuwa watan Afrilu 2026, inda duk wanda bai bi ƙa’ida ba zai iya fuskantar hukunci, lamarin da ke nuna sabon mataki a kula da kasuwar rance a dijital da ke ƙara bunƙasa a ƙasar.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Masana Sun Goyi Bayan Amfani Da AI Wajen Tantance Rajistar Masu Zaɓe
  • Abubakar Sulaiman
    Yadda Masu Amfani Da Wema Bank Za Su Duba Cancantar Samun Tallafin 50,000
  • Abubakar Sulaiman
    Ku Daina Amfani Da Kotu Wajen Hana Mu Takara A 2027 ADC Ga APC
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴansanda Sun Kuɓutar Da Shugaban APC Na Rogo Bayan Shafe Kwana 68 A Hannun Masu Garkuwa

MASU ALAKA

Yawaitar Tashin Gobara A Kasuwannin Kano, Shin ’Yan Kasuwa Na Samun Kulawar Da Ta Dace?
Labaran Kasuwanci

Yawaitar Tashin Gobara A Kasuwannin Kano, Shin ’Yan Kasuwa Na Samun Kulawar Da Ta Dace?

November 2, 2026
Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Jawo Hankalin Masu Zuba Jari Daga Ƙasashe 120
Labaran Kasuwanci

Hannun Jarin Matatar Dangote Ya Jawo Hankalin Masu Zuba Jari Daga Ƙasashe 120

October 28, 2026
Rusau A Kano: Sarki Sanusi Ya Roƙi Abba Ya Biya ’Yan Kasuwar Filin Idi Diyya
Labarai

Rusau A Kano: Sarki Sanusi Ya Roƙi Abba Ya Biya ’Yan Kasuwar Filin Idi Diyya

October 18, 2026
Next Post
Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Shaida Yadda Fina-finai Na Sin Ke Haskakawa Duniya Ainihin Kasar Sin

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Shaida Yadda Fina-finai Na Sin Ke Haskakawa Duniya Ainihin Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Yawancin Kiristocin Da Muka Tattauna Sun Gamsu Da Tikitin Muslim-Muslim – Yilwatda

Yawancin Kiristocin Da Muka Tattauna Sun Gamsu Da Tikitin Muslim-Muslim – Yilwatda

November 10, 2026
’Yan Majalisa Ne Za Su Yanke Hukunci Kan Makomar Akpabio – Shugaban Jam’iyyar APC

’Yan Majalisa Ne Za Su Yanke Hukunci Kan Makomar Akpabio – Shugaban Jam’iyyar APC

November 10, 2026
’Yansanda Sun Ceto Mutane 2 Da Aka Sace Tare Da Lalata Maɓoyar ’Yan Bindiga A Sakkwato

’Yansanda Sun Ceto Mutane 2 Da Aka Sace Tare Da Lalata Maɓoyar ’Yan Bindiga A Sakkwato

November 10, 2026
2027: Wike Ya Yi Alƙawarin Bai Wa Kowane Kansila A Abuja N10m Idan Ya Tabbatar Da Nasarar Tinubu

2027: Wike Ya Yi Alƙawarin Bai Wa Kowane Kansila A Abuja N10m Idan Ya Tabbatar Da Nasarar Tinubu

November 10, 2026
Gwamnan Neja Ya Rera Waƙoƙin Kiristanci A Wajen Wani Taro

Gwamnan Neja Ya Rera Waƙoƙin Kiristanci A Wajen Wani Taro

November 10, 2026
2027: NDC Za Ta Samar Da Gwamnatin Da Za Ta Yi Tafiya Da Kowa – Kwankwaso

2027: NDC Za Ta Samar Da Gwamnatin Da Za Ta Yi Tafiya Da Kowa – Kwankwaso

November 10, 2026
INEC Ta Cire Rijistar Masu Zaɓe Miliyan 1.6 Da Ba Ta Inganta Ba

INEC Ta Cire Rijistar Masu Zaɓe Miliyan 1.6 Da Ba Ta Inganta Ba

November 10, 2026
Gwamnatin Abba Kabir Za Ta Inganta Tsarin Makarantun Tsangayu A Kano – Falaki

Gwamnatin Kano Za Ta Kula Da Lafiyar Shugaban APC Da Aka Ceto Bayan Shafe Kwanaki 68 A Hannun ’Yan Bindiga

November 10, 2026
Kasar Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Intanet

Kasar Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Intanet

November 9, 2026
’Yansanda Sun Kai Samame Maɓoyar ’Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane Biyu a Sakkwato

’Yansanda Sun Kai Samame Maɓoyar ’Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane Biyu a Sakkwato

November 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.