ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Rashin Biyan Bashi Tsakanin Surukai Ke Shafar Zamantakewar Aure

by Rabi'at Sidi Bala
8 months ago
Aure

Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zaƙulo muku batutuwa daban-daban waɗanda suka shafi al’umma. Ciki sun haɗar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.

Tsokacinmu na yau zai yi duba game da abin da ya shafi rancen kuɗi/bashi tsakanin surukai, duba da yadda irin wannan matsalar ke taka rawar gani wajen lalacewar zamantakewar aure tsakanin ma’aurata. Wasu iyayen kan rufe ido su je wajen mijin ‘yarsu domin karvar bashi, wanda hakan na faruwa ne tsakanin uba da kuma uwar yarinyar.

Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu; “Shin hakan ya dace ko kuwa, kuma me yake janyo hakan?, Ko akwai wasu matsaloli da hakan ke iya haifarwa, musamman ga ita yarinyar?, Ta wacce hanya ya kamata a fahimtar da masu aikata hakan?.

ADVERTISEMENT

Ga dai bayanan nasu kamar haka:

 

LABARAI MASU NASABA

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?

Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?

Sunana Aminu Adamu Malam Madori A Jihar Jigawa:

Eh tabbas hakan yana faruwa ga wasu iyayen da basa jin kunyar surukansu, da kuma rashin sanin mutuncin kai dama mutuncin yar. Babu wani dalili da zai sa ka rasa gurin da za ka yi aron kuɗi sai surinkin ka. Matsaloli na da yawa kamar, zubar da mutuncin ‘yarka da mutuncinka. Kuma hakan na iya jawo matsalar zamantakewar gidan auren ga ‘yar ka, musamman idan tana da abokiyar zama. Hnyar da za a fahimtar da masu irin halin, a fito fili a gaya musu gaskiya su san abin da suke bai dace ba tare da nusantar da su illolin hakan.

 

Sunana Hauwa Abubakar Sarki, daga Jihar Neja:

Da fàrko zan iya cewa rashin sanin daraja da son banza ne ke janyo haka. Domin ni ban ga dalilin da zai sa na je wajan mijin ‘ya ta neman rancen kuɗi ba. Duk masu irin wannan halin su daina, domin hakan ba tsari bane. Matsala kuwa darajarta da kimarta zai ragu a idon mijinta, dama ‘yan’uwansa ko abokai idan ya labarta masu. A fahimtar dasu da kuma nuna masu illar hakan da abun da zai janyowa ‘yar tasu a zamantakewar aurenta.

 

Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Rano A Jihar Kano:

Ya dace mana, saboda wasu surukan suna ɗaukar mazajen yaran nasu matsayin yaransu ne, suna gudun kada su je wani wajen a yarfa su. Wasu kuma son zuciya ne, ganin cewa ko da basu biya ba, ba za a takura musu ba. Matsaloli; gori zai iya shiga tsakani da kuma cin fuskar ita yarinyar daga wajen mijin nata da ‘yan’uwan mijin. Hanayra magancewa, yarinyar ta riƙa faɗawa baban nata illar hakan, shi ma uban ya riƙa sanin yakamata.

 

Sunana Hafsat Sa’eed, daga Naija:

A nawa ganin hakan babu girma a ciki, surika ko suriki ya riƙa bin suriki rancen kuɗi ai babu girma, bai dace ba kwata-kwata saboda surikan zamani a yadda suke yanzu babu abin da ba za su iya yi ba. Matsaloli sune; Raini, cin mutunci, gori wajen miji, da sauransu. Hanyar magancewa, babu aro tsakaninka da suriki.

 

Sunana Muhammad Isah Zareku, Miga, A Jihar Jigawa:

A gaskiya hakan na faruwa, amma ba laifi bane ka ranci kuɗin suriki. Abin da yake janyo hakan shi ne, rashin wadata a wajen surikin, to, kuma ai taimakekkeniya ce hakan, idan ka samu ka mayar masa kuɗinsa. Ba wani matsala idan har mijin yarinyaar yana son taimakon iyayen matar tasa. A duk lokacin da mutum ya ranci kuɗin ka ai za ka samu lada me yawa, kuma idan ya dawo ma dashi lokacin kai ma za ka ji daɗi.

 

Sunana Princess Fatima Mazadu, Jihar Goben Nijeriya:

Wani zubin talauci ne, wasu lokutan kwaɗayi da zubda mutunci da siyawa kai raini mai tsanani. Wasu surukan ma baka tambaye su ba sun gama raina surukansu bare kuma an sa su gaba da karvar bashi. Ba shi da amfani, saboda zubar mutuncin surkuntaka da ɗiyar su bakiɗaya. Talauci ne da kuma rashin haƙurin rayuwa, akan wata buƙata. Matsalolin sune; raini, zubar kima da mutunci, rashin ganin girman juna, rashin yarda da dai sauransu. Idan an ce maka suriki to, an sanyo alkunya da girmamawa ne.

 

Sunana Alhassan Abdulrahman Bununu, Tafawavalewa Jihar Bauchi:

Ba daidai ba ne surika ta riƙa karvar rancen kuɗi a gun mijin ‘yarta dan hakan na’iya jawo mata rashin kima da daina ganin girmanta a wajen surkin nata. Kuma hakan na iya janyo wa yarinyar rashin martabawa wajen mijin dama danginsa. Matsalolin da hakan ke haifarwa shi ne bata isa ta ce wani abu ba, in har wani abu ya haɗa su na rashin fahimta ko da kuwa cin zarafin iyayen ake yi bata isa ta rama ba. Ita yarinyar ta faɗa musu gaskiya akan hakan.

 

Sunana Aisha T. Bello, daga Jihar Kaduna:

Gaskiya rancen kuɗi a hannun suriki kwata-kwata bai kamata ba. Hakan kamar wani nau’i na roƙo ne a kaikaice a gani na. Sannan hakan zai haifar da raini babba da zubar mutumci a idon surikin. Kuma zai zubar wa ɗiyarsa kima da mutunci. Ko da mijin ya yi wa ‘yar wani abu, iyayen ba za su iya ɗaukar mataki ba. Masu hakan don Allah su cire son zuciya, su sayawa yaransu mutumci, son zuciya ne duk ke haifar da hakan. Iyaye na taka rawa mai girma a rayuwar auren yaran su. Idan suka zama mutanen kirki da ababen koyi, to wallahi sun saya mata girma a idon miji dama kowa. Na gode da bani dama a wannan jarida mai albarka don tofa nawa tsokacin akan wannan maudu’in.

 

Sunana Muktari Sabo, Jahun, Jihar Jigawa:

Tabbas ana samun iyaye masu irin wannan ɗabi’a kuma hakan ba girmansu bane, bai dace ba, rashin kare mutuncin kai ne. Hakan zai iya janyowa yarinyar rashin kima da daraja. Hanyar magance wa, ka da yarinyar ta bari hakan ta faru domin galibi ta gurinta za a fara biyo wa dan neman rancen to, ka da ta buɗe ƙofar hakan.

 

Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos, a Jihar Filato:

Wani abu da na daɗe ina jan hankalin matasa masu shirin aure da sauran maza masu niyyar ƙarin aure shi ne, su guji yin gaggawa wajen neman aure, kuma su tabbatar da sun yi bincike sosai, ba kawai ga rayuwar wacce za su aura ba, har ma da halayen iyayenta da ‘yan’uwanta, domin gudun ɗaukar kara da kiyashi. Kuskure ne babba mutum ya yi aure ido rufe, ba tare da ya san me ya aura, ko kuma daga ina ya aura ba. Don a gaskiya wasu surukan ban da abin takaici da abin kunya babu abin da suka iya, ga zubar wa ‘ya’yansu mutunci a wajen mazajensu. Ga koyawa ‘ya’yansu cin amanar aure, rashin riƙe sirrin aure, takura wa miji, da hana shi kwanciyar hankali. Har akwai iyayen da suke koya wa ‘ya’yansu mata sata ko damfarar miji, don su kai musu kuɗin gida.

 

Sunana Jibrin Yusuf Kaila, daga Jihar Jigawa:

A tsarina al’adar Malam Bahaushe bai kyautu ba, don ba a saba ganin haka ba, kuma babu daraja. Amma yau da gobe babu wanda bata bari ba, domin bashi hanji ne, kowa yana da shi. Ba laifi ba ne duk da ba a saba gani ba, amma yau da gobe ce take sa wasu abubuwan suke faruwa saboda hali na yau. Batu na gaskiya, iyaye masu irin wannan halin kan ja wa yaransu mata abin gori a gun dangin miji, musamman ƙannen miji, don abin gori ba ya yi wa mata kaɗan. Daga ƙarshe ya jawo wa yarinya matsala a zaman aurenta.

Aure
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Alaƙata Da Adamu Zango Ta Bunƙasa A Kannywood —Jarumi Ibrahim Sodangi 
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim Ko Gaske:Yaushe Masu Kallon Fina-finai Za Su Daina Daukar Fim A Matsayin Gaske
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Fim ɗin ƙaddara: Anya Ana Samun Irin Wannan ƙaddarar Kuwa?
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ko Kafa Ƴansandan Jihohi Zai Taimaka Wajen Kawo Ƙarshen Matsalolin Tsaro?

MASU ALAKA

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?
Taskira

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?

September 5, 2026
Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?
Taskira

Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?

August 29, 2026
Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?
Taskira

Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?

July 25, 2026
Next Post
Tinubu Ya Saita Wa Gwamna Yusuf Hanyar Sauya Sheƙa Zuwa APC

Ƙwace Mulki A Hannun Tinubu Ne Kaɗai Hanyar Ceto Nijeriya A 2027 — ADC

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.