Mugun Lodi Ya Janyo Kifewar Kwalekwale Dauke Da Mutum 160 A Kebbi  

Daga Abubakar Abba da Umar Faruk,

A jiya Laraba ne, wani kwalekwale ya kife da wasu fasinjojin da aka yi mugun lodi da su tare da kaya masu nauyi a yankin Jihar Kebbi.

Kwalekwalen dai ya kife ne a Kogin Neja dauke da fasinjoji kimanin 160.

Da yake karin bayani kan lamarin, Shugaban karamar Hukumar Warra-Ngaski ta Jihar Kebbi wanda al’amarin ya faru a yankinta, Abdullahi Buhari ya bayyana cewa jirgin ya taso ne daga Neja ta tsakiya zuwa Jihar Kebbi a yayin da lamarin ya auku.

Ya ci gaba da cewa, a yanzu haka (lokacin da yake magana), fasinjojin  22 ne suka tsira,  daya kuma ya rasu wanda an gano gawarsa.

 

Wara ya kara da cewa, “A yanzu haka da muke yin magana da ku, kimanin fasinjojin 140 sun bace har yanzu ba a gansu ba, inda kuma ya dora laifin yin hadarin ga yawan lodin da ya wuce iyaka da aka yi wa kwalekwalen wanda kamata ya yi a ce, ya dauko fasinjoji 80 kacal.”

Ya bayyana cewa an kuma loda wa kwalekwalen manyan kaya da suka hada da buhunan shinkafa ‘yar kasa da aka dauko daga inda ake hakar na’adanai.

A cewarsa, a farkon wannan watan kimanin fasinjojin 30 suka nutse a kogi sakamakon hadarin jirgin ruwa yankin Ne-a ta tsakiya cikin Jihar Neja.

A cewar wasu jamai’ai,  Kwale-kwalen wanda  ya dauko fasinjiji 100 ‘yan kasuwa ya shige gida biyu bayan da ya yi karo da dutse.

Haka zalika da yake magana da wakilinmu Sarkin Samarin Warra Adamu Umar ya bayyana cewa mutanen sun kusan 200 wadanda suka nutse. Sannan shi da kansa ya kirga gawa guda hudu daga cikin wadanda ceto.

Exit mobile version