Muhimmancin Koya Wa Yara Sana’a

Sana'a

A yau zamu tattauna ne a kan sana’a, yadda za mu nema wa yaranmu abin yi a lokacin da aka kai su dakin miji. Iyaye mata da yawa kan yi wani kuskure wurin tura yara mata gidan miji ba tare da kwakkwarar sana’a ba. Haka a lokacin saya musu kayan daki maimaikon tarin kayan kawa yana da kyau mu saya musu abin sana’a , misali kamar keken dinki, fridge da generator, kayan electronics na gasa cake da sauran nau’in abubuwan gashe gashe.

 

Tun farko a zauna da miji a tattauna batun cewar yarinya za ta yi sana’a bayan aure. Hakan zai taimaka matuka wurin dorewar zaman aure. Sannan kuma a wurin yin sana’ar nan ba kawai za a nuna mata yin sana’ar kawai ba ne ta wofintar da abin da ya shafi kulawar gidanta da mijinta ba. A koya mata tsara lokutan da take yin sana’a da kuma lokacin da za ta bawa mijinta kulawa, da yadda za ta kula da al’amuran cikin gidanta. Yawan mace-macen aure da matsalollin aure da ake samu a yanzu ba zai rasa nasaba da rashin sana’a ba. Kasancewar a yanzu rayuwa ta yi tsada ana bukatar hadin gwuiwa ko tallafawa a tsakanin ma’aurata.

 

A yanzu an wuce iyaye su tara wa yarinya kayan duniya a dakin miji kuma a bar ta ba ta da abin yi ba. In tana da sana’a mijin ma zai fi ganin kimarta auren kuma zai fi yin karko saboda zai rage yawan tambayar miji musamman a lokutan da ba shi da shi.

 

A wannan zamani rashin sana’a na taka muhimmiyar rawa wurin haifar da matsala a cikin al’umma. Maza da mata yana da kyau mu sama musu abin yi bayan sun dawo daga makaranta, ta haka yaro zai tashi ya san kima da darajar duk abin da ya samu. Iyaye da yawa kan manta koya wa yaro sana’a har ya girma, a lokacin da ya girma kuma abin sai ya zama masa da wahala.

 

Musamman yara mata da ake aurar da su ba tare da wata sana’a ba. Ita sana’ar nan ba dole sai kayan kudi har can ba, ko misalin dubu biyu ko uku akwai abin da mace za ta sara ta sayar har ta ci riba, kun ga a nan ko katin waya ta sauwaka wa kanta a kan sai miji ya bata. Mafi aksarin matsalolin da ke tasowa a gidan aure har da talauci, idan mace na da hanyar samu to dole za ta tallafawa kanta da wani abu.

 

Sannan yana da kyau iyaye idan sun tashi aurar da yarinya maimakon kayan karau da za a jibge mata, kamar yadda na fada a baya, zai fi kyau a saya mata fridge da genarator ko keken dinki ko na saka, a dunkule ta yi ta sana’a da shi. Idan kuma yarinya mijin ba mazauni ba ne tafiya zai yi da matar, kar a je a jibge kaya a gida ba kowa karshe ma in ba a dace ba barayi su shigo su kwashe, an yi asara bakidaya. Abin da ya fi sai a sayar da kayan a saya mata gida ko fili wanda duk lokacin da za ta dawo zama wuri daya za ta daga kayanta ta sayar ta samu abin dogaro da kanta, kuma hakan zai rage matsalolin gidan aure matuka.

Allah ya sa mu gyara.

 

Exit mobile version