Mujallar Qiushi Za Ta Buga Muhimmin Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Ciyar Da Ilimi, Fasaha Da Kwararru Gaba Tare”Za a buga muhimmin sharhin babban sakataren jam’iyyar kwaminis ta Sin, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, mai taken “Ciyar da ilimi, fasaha da kwararru gaba tare” a cikin mujallar Qiushi fitowa ta 12 da za a buga a ranar 16 ga watan Yuni.Sharhin ya nuna cewa, ya kamata a karfafa tallafin aikin ba da ilimi ga fasaha da kwararru, da kuma gaggauta horar da ingantaccen rukunin kwararru masu shafar bangarori daban-daban, dake iya yin kirkire-kirkire. (Amina Xu)
ADVERTISEMENT















Discussion about this post