Shugaban ƙungiyar Masu kishin gyaran dimokuraɗiyya a arewacin Nijeriya Malam Ibrahim Shekarau ya koka kan yadda yankin Arewa ke cigaba da zama koma baya a Nijeriya.
Hakan ya biyo bayan yadda yankin yake fama da matsalolin da suka ƙi ci suka ƙi cinye wa kamar matsalar tsaro da bara da yunwa da kuma yadda ake zaɓar shugabanni a yankin. Tsohon gwamnan na Kano ya bayyana hakan ne yayin wata zanta wa da kafar BBC Hausa.
- 2027: Ko Sabon Yunkurin Su Shekarau Zai Kai Arewa Ga Gaci?
- Shekarau Ya Fara Jagorantar Sabuwar Tafiyar Kawo Sauyi A Nijeriya
Ya ce irin wannan matsalolin ne ya sa suka kafa wannan ƙungiya bayan dogon nazari da tuntuba don samar da mafita.
Mallam Shekarau ya ce
“Mun fi shekaru biyu muna tattauna kan yadda kasa ta lalace, yadda ake zaben shugabanin ya lalace, yadda aka mayar da zaɓe dauki dora, da koma baya da ake fama da shi a fanin hadin kai yasa muka yanke hukuncin daukar mataki na kawo gyara a wannan ɓanagare”
in ji shi.
Daga cikin irin abubuwan da wannan tafiya zata mayar da hankali sun haɗa da samar da haɗin kan al’umma, da bayar da ingantacen ilimi musamman ganin irin gorin bara da almajirci da ake yi mana, wanda da mun tsaya mun ɗauki matakin da ya kamata da tuni mun yi nisan da ya kamata, a bangaren ilim, da kuma sauran matsaloli da yankin namu ke fama da shi”
Akwai irin waɗannan ƙungiyoyi da dama a yankin Arewa amma har yanzu babu wani tasiri da suka yi da za a iya nuna wa wajen warware matsalolin yankin, lokaci zai yi a gaba da za a iya gane ko wannan tafiya irin sauran ce ko kuma zata yi nasara kan ƙudirinta.