Abdullahi Alhassan" />

Mun dade Muna Jiran Bayyana Takarar Buhari – Kano APC

Daga Abdullahi Alhassan

Jam’iyyar APC ta Jihar Kano ta bayyana cewa, sun dade suna jiran Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana kudirin sa na sake tsayawa takara a zaben shekara ta 2019.

Mataimakin Shugaban jam’iyyar  APC ta Jihar Kano, Alhaji Shehu Maigari, ya ce, fadar Buhari ba ta zama abin mamaki ga ba a wurin su. A cewar sa jam’iyyar APC ta Kano ta amince da ya sake tsayaw takarar tun lokacin da ya kai ziyarar aiki ta kwana biyu a jihar a bara.

“Mutanen Kano sun amince da Buhari don sake tsayawa takarar sa’annan tun daga nan muke jira bayyanawar sa. Mun gode wa Allah cewa shugaban  Buhari ya amsa kiranmu. ”

Maigari ya bayyana cewa, babban mataki na rashin tsaro da cin hanci da rashawa da jam’iyyar PDP ta yi na tsawon shekaru 16, ba za a iya magance shi ba idan har sai Buhari ya wadataccen lokaci dan ya ci gaba da ci gaba da tsarinsa na farfado da tattalin arziki, dakile cin hanci da rashawa da kuma murkushewa da magance matsalolin tsaro.

Maigari ya kara da cewa mafarkin Nijeriya na zama kasa mai dogara da kanta a game da samar wa kanta abinci zai iya zama gaskiya idan an yarda da ci gaba da mulki.

Saboda haka, Mataimakin Shugaban ya yi kira ga jama’ar Kano da ‘yan Nijeriya baki daya da su ci gaba da goyon bayan gwamnatin Buhari.

Exit mobile version