Mun Samu Nasarori Da Dama Cikin Shekara 6 Fiye Da Shekara 16 Na PDP, Inji APC

APC

Daga Sulaiman Ibrahim

Wasu shugabannin jam’iyyar APC mai mulki sun ce gwamnatin da Shugaba Muhammadu Buhari ke jagoranta ta samu nasarori cikin shekaru shida fiye da gwamnatocin da suka gabata a karkashin jam’iyyar PDP tsakanin 1999 zuwa 2015 idan aka kamanta su.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun tsohon Sakataren yada labarai na Jam’iyyar APC na kasa, Mista Lanre Issa-Onilu, wanda shi ne Shugaban kungiyar ci gaban Gwamnoni (PGF) na yanzu; Salihu Mohammed Lukman; Babban Mataimaki na Musamman kan Shirin jin kai ga Shugaba Buhari, Barr. Ismail Ahmed; da Mataimaki na Musamman kan watsa labarai ga Buhari, Mista Tolu Ogunlesi.

Jiga-jigan APC, wadanda suka sanar da fara yakin neman zabe na kasa don inganta manufofin Shugaba Buhari gabanin babban zaben shekarar 2023, sun ce manufar ita ce gabatar da nasarorin gwamnatin tare da zube hujjoji akan nasarar.

Exit mobile version