Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ta kaddamar da shirin tara kudade ga jama’a domin yakin neman zaben dan takarar gwamnanta na jihar, Abba Kabiru Yusuf wanda aka fi sani da “Abba Gida”.
A wajen taron liyafar cin abinci na musamman da jam’iyyar ta shirya domin samun tallafin kudi daga ‘ya’yan jam’iyyar, NNPP ta ce an samu sama da Naira miliyan 511, wanda kaso mafi tsoka ya fito ne daga dan majalisa mai wakiltar Tofa/Dawakin-Tofa/Rimin-Gado a zauren majalisar wakilai Tijjani Abdulkadir Jobe wanda ya bada gudunmawar Naira miliyan 50.
- Duniya Ta Shiga Alhinin Mutuwar Sama Da Mutum 3,000 A Turkiyya Da Siriya
- An Gurfanar Da ‘Yan Bangar Siyasa 10 A Gaban Kotu A Sakkwato
Da yake jawabi a wajen liyafar, shugaban masu bayar da tallafi kuma tsohon mai taimaka wa shugaban kasa, Abdulrahman Kawu Sumaila ya bayyana cewa NNPP ta himmatu wajen fara yakin neman zabe da goyon bayan mambobin jam’iyyar.
Tsohon dan majalisar wakilan, ya karyata zargin sayen kuri’u da magudin zabe sannan ya kara da cewa jama’a sun taru ne domin su bayar da nasu tallafin.
Sumaila ya kara da cewa ’yan jam’iyyar NNPP masu sadaukarwa ne saboda suna da akidar Kwankwasiyya da ba ta da kudi.
Ya kara da cewa NNPP ta shirya tsaf domin kwato Kano daga jam’iyyar APC mai mulki a zaben gwamna da za a yi a wata mai zuwa.
“Zabe na karatowa kuma NNPP ba ta buri face kwato Kano. Mun taru a matsayinmu na NNPP da iyalan Kwankwasiyya don tattara kayan aiki don yakin neman zaben gwamna,” in ji Sumaila.
“Yanzu, cikin kasa da sa’o’i uku, mun samu tallafin jama’a sama da Naira miliyan 500 kuma har yanzu muna ci gaba da karbar tallafin. Kamar yadda kuka sani ba ma cikin gwamnati don haka ba mu da wani gata da asusun gwamnati don haka ne muke bude wannan taron jama’a inda muka nemi tallafi.
Dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf, ya yaba da goyon bayan mambobin da suka bayar da gudunmawarsu, inda ya ce NNPP ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da ayyukan al’umma idan har aka zabe su.