A daidai lokacin da al’ummar Nijeriya suka yi ban kwana da shekarar 2022 da abubuwan da suka faru a cikinta a bangaren siyasa, tsaro, tattalin arzki da kuma zamantakewa, sun kuma bayyana irin fatan da suke da shi a sabuwar shekarar 2023 a bangarori da dama, musamman gannin a cikin shekarar ne za a fuskanci zaben sabuwar gwamnati, gwamnatin da za ta fuskanci kalubale da dama a bangaren tsaro siyasa tattalin arziki da sauransu. Wakilanmu daga sassan kasar sun tattauna da wasu ‘yan Nijeriya inda suka bayyana irin fatan da suke da shi a sabuwar shekarar.
Jihar Yobe
Ranar Lahadi ce ta dace da ranar farko a sabuwar shekarar 2023; sakamakon ban-kwana da aka yi da shekarar 2022. Ya yin da bisa ga al’ada, kowace shekara jama’a kan yi kyakkyawan fata tare da dimbin buri dangane da muhimman abubuwan alhairin da kowace sabuwar shekarar ta kunsa.
Wakilinmu a jihohin Borno da Yobe ya jiyo ra’ayoyin jama’a dangane da abubuwan da suke buri tare da fatan abkuwar su a cikin wannan shekara ta 2023, wanda suka shafi al’amurran siyasa, bunkasar tattalin arziki da magance matsalolin tsaro wadanda suka fi ciwa yan Nijeriya tuwo a kwarya.
A nashi ra’ayin, Mallam Mohammed Dalah Lawan ya ce babban burin da yake dashi a wannan shekara ta 2023 shi ne; “Da yake a wannan shekarar ne zamu zabi sabuwar gwamnati a matakin tarayya da jihohi, muna so gwamnatoci su mayar da hankali kan matsalolin tsadar rayuwa, wanda shi ne al’amari mafi tasiri a rayuwar yan Nijeriya. Saboda duk inda ka mika hannunka babu dadi, talakawa muna cikin mawuyacin hali kan yadda farashin kayan abinci da na masarufi ke hauhawa kullum, muna fata tsadar ya ragu.”
Ya kara da bayyana cewa, “Musamman idan an yi la’akari da yadda daminar bana ta zo da mummunan ibtila’in ambaliyar ruwan da ya barnata amfanin gonakin jama’a. Wanda hakan ya jawo karancin abinci, sannan suma sauran kayan masarufi gasu nan ba a cewa komai sai dai addu’a. Saboda haka a matsayin mu na yan Nijeriya muna so shugabanni su kalli wannan fanni tare da daukar matakan kawo sauki ga jama’a.”
Mohammed Dalah ya kara da cewa, baya ga hauhawar farashin kayan abinci da na masarufi, muna so sabuwar gwamnatin da za ta zo ta duba bangaren tattalin arziki, sashen da yake cike da kalubalen da ya dace a tallafa don ya bunkasa. Sannan bunkasa sha’anin tattalin arziki zai taimaka wajen rage tsananin rayuwa wanda matsalolin tsaro suka haifar a wannan yanki namu na Arewa Maso Gabas.
A nashi bangaren, Alhaji Ibrahim Gurugusko (Tafidan Tikau) ya ce, “Da farko muna murna da shiga wannan sabuwar shekara ta 2023, kuma ina fatan a samu nasarar gudanar da manyan zabukan da muka saka a gaba lafiya a wannan shekara. Kuma ina da burin gwamnatin Jihar Yobe ta canja yadda take tafiyar da harkokin ayyukan noma tare da sauyin yadda take daukar manoma a Jihar Yobe. Wanda muna burin a wannan shekara gwamnatin jihr Yobe ta dauki matakan inganta ayyukan noma sabanin yadda suke a baya; babu takin zamani, babu tallafi ga manoma.”
“Sannan duk da albarkatun dabbobi da muke dasu, gwamnati bata bayar da muhimmanci ga taimakon makiyaya a fannin samar musu wuraren kiwon dabbobi mai inganci tare da ruwan sha. Haka kuma muna fata a wannan sabuwar shekara gwamnatin jihr Yobe ta sanya ido wajen dakile matsalolin rikici tsakanin makiyaya da manoma.”
Dr. Umar Goni na Jami’ar Maiduguri ya bayyana cewa, babban buri da fatan kowane dan Nijeriya a wannan sabuwar shekara shi ne samun canjin da aka dade ana fatan a samu bai samu ba. Ya ci gaba da cewa, “Fatan dukanin yan Nijeriya shi ne a samu canjin a harkar ilimi, noma, zamantakewa, tsaro, kana da fatan samun saukin rayuwa wajen saukowar farashin kayan abinci da na masarufi.”
“Sannan kuma wadannan abubuwan za su samu ne ta hanyar Shugaba nagari, wanda yake da tausayin al’umma a zuciyar shi kuma mai karfin ikon sauya al’amurra zuwa inganta rayuwar yan kasa baki daya. Wannan shi ne burin kowane dan Nijeriya a wannan zabe mai zuwa; ba tare da kama suna ba, muna so Allah ya sa a samu sabbin shugabanin da za su zo su zama nagari.” Ya bayyana.
Jihar Kano
Abubuwan da Gwamnati ke yamadidin cewa an samar da nagartattun hanyoyin Inganta tattalin arziki lamarin be dake cike da laije a cikin nadi, Kwamared Ishak Ganduje Albasa guda ne cikin masu yawan yin fashin baki Kan Harkokin tattalin arziki ne ya bayyana haka ga Jaridar Leadership hausa kan yadda masana ke kallon yadda wannan Sabuwar Shekarar zata Kasance musamman ta fuskar tattalin arzikin Kasa.
Gandun Albasa ya ce, da yawa wasu abubuwan da Hukumomin ke fada kan batun tattalin arziki, babu shakka basu dauko hanyar inganta shi ba. ya bayar da misalin da batun canjin kudin da akayi, Wanda yace yanzu haka Talakawa ma tsoron wadannan sabbin kudaden suke, haka suma bankunan ba suda isassun wadannan sabbin kudade, sannan Nijeriya na fama da gagarumar matsalar rashin ingantaccen tsarin Network wanda hakan ke.hana ingantuwar tsarin ta’ammalin da kudade ta yanar gizo
Dakta Ali Ado Siro, Malami ne a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa, sannan Kuma malami ne a fannin Nazarin manyan Laifuka, ya bayyana cewa batun tsaro a kasarnan matakan da ake cewa an dauka, alokuta da dama matakai ne da suke da alaka kai tsaye da siyasa, domin alokuta daban daban zaka hi Shugaban Kasa na shelanta fitar da makudan kudade Kan batun tsaro, amma ba inda ya kamata su kudaden ke zuwa ba.
Dakta Siro ya ci gaba da cewa dole sai mahukuntan sun tauna tsakuwa domin aya taji tsoro, a daina amfani da siyasa ta fuskar kokarin magance matsalar tsaro.
Shekara ta 2023 Shekara ce da ake kyautata zaton samun sauyi ta fuskar zabar nagartattun Shugabanni. Alhaji Safiyanu Ibrahim Gwagwarwa (Tafidan Gwagwarwa) ne ya bayyana haka alokacin da yake tsokaci kan mahangar masana kan siyasar Shekara ta 2023.
Tafidan Gwagwarwa yace duba da yadda ake kara samun nutsuwa ga masu zabe ta fuskar ‘yan takarkarun da suka fito daga sama har kasa, alamu sun bayyana za’ayi siyasar ‘yanci tare da zabar nagartattun Shugabanni, musamman mu a Jihar Kano, ko hasidin iza hasada ya gamsu da nagartar dan takarar kujerar Gwamna na Jam’iyyar APC Dakta Nasiru Yusif Gawuna, wanda aduk farfajiyar siyasar Kano bashi da abokin hamayya, shi kowa nasa ne, sannan shi ne kullum ke jan hankalin magoya baya da su guji siyasar daba da batanci. Inji Gwagwarwa.
Jihar Kebbi
A jin ra’ayin jama’a daga Jihar Kebbi kan lamarin tsaro, tattalin arzikin kasa da kuma zabe Mai karatowa a cikin sabuwar shekarar 2023 da muke ciki.
Wakilinmu ya samu zantawa da wani tsohon jami’in tsaron ‘yan Sanda Mai suna Aliyu Shehu Birnin Kebbi wanda ya yi ritaya a matsayin mataimakin kwamishinan ‘yan Sanda ya ce” jama’a na bukatar a Samar musu da tsaro mai inganci wanda zai taimaka wajen gyaran tattalin arziki kasa da kuma gudanar da sauye sauye a duk hukumomin tsaro na kasar idan ana son tsaro ya inganta har ‘yan kasa su samu gamsu wa, inji shi”.
Haka kuma ci gaba da bayyana cewa “daya daga cikin inganta tsaro dole ne a Samar da kayan aiki na zamani ga hukumomin tsaron kasa da ba da kyakyauwar kula da walwala da kuma jinda din Ma’aikatan tsaro don kawar da zukatansu ga cin hanci da rashawa ya yin gudunar da ayyukan su na Samar da tsaro ga kasa.
Bisa ga hakan muna saran shugabanni da za a zabe a nan gabata kadan za su mayar da hakali ga gyaran tsaro, tattalin arzikin kasa da gyaran tsarin mulkin kasa ta yadda ‘yan kasa za su samu gamsu.
Kazalika wani malamin Jami’ar gwamnatin tarayya da ke Birnin Kebbi a sashen nazari da karatun ilimin tattalin arzikin kasa Mai suna Dakta Bashir Abubakar ya ce “akwai kalubale ga tattalin arzikin kasa wanda akwai bukatar samun shugabanni wadanda da za su iya gyaran tattalin arzikin kasa domin tabarbarewar tattalin arzikin a kasar nan ya haifar da abubuwa da yawan a cikin kasa da kuma ga ‘yan kasa. Daga cikin abin da ke iya biyo wa baya kan tabarbarewar tattalin arzikin a kasa shi ne rashin abinci da rashin tsaro. Bisa ga haka ya zama wajibi ga shugabanni su kula da tattalin arzikin kasa da na jahohi. Haka kuma idan jama’a na zabe su tabbatar da sun zabi shugabanni da ke da ilimi akan inganta tattalin arzikin kasa da na jahohi don ta hakan ne kawai al’ummar kasa ke iya tsayawa bisa kafafunta.
Har ilayau wakilinmu ya zanta da wani dan siyasa Mai suna Umaru Bande (kansila) wanda ya bayyana siyasa wata dama ce da dokar kundin tsarin mulkin kasa ta baiwa jama’ar kasa don samun damar zaben shugabanni da kuma samun ‘yancin kai da fadin albarkacin bakin su da kuma cin gajiyar damokradiyya ta hanyar gudanar da ayyukan da jama’a ke bukata da kuma samar da aikin yi ga ‘yan kasa. Saboda haka a wannan siyasa mai karatowa na shekara 2023 da muke ciki muna bukatar shugabanni da za su samar da ingantacen tsaro da gyaran tattalin arzikin da kuma da damar shigar da ‘yan kasa ga shugabkncin al’ummar jihohin kasar nan. Ina kuma kira ga jama’a a ya yin yakin neman zabe da su guji tashi hankali musamman matasan jahohin kasar nan da ke bari wasu ‘yan siyasa na amfani dasu wajen biyan muradun su na siyasa.
Jihar Neja
Ra’ayoyin jama’a kan sabuwar shekarar 2023, shugabn kungiyar kiristoci na kasa reshen Jihar Neja, Dokta Bulus Dauwa Yohana (Rabaran) ya ce ” Ya kamata al’ummar su kaunaci juna, ta hanyar taimakon mabuka da kishin kasa. Domin littafi mai tsalki ya tabbatar mana al’umma na samun cigaba ne ta hanyar tausayawa mabukata musamman wannan lokacin mai muhimmanci, na sabuwar shekara, sakamakon kalubalen rashin tsaro da jama’a suka sha wahala a shekarar da ta gabata.
Dr. Bulus, ya nemi al’umma su yi anfani da koyarwar littafi mai tsalk wajen hadin kai, zaman lafiya da nuna kauna ga abokan zama, domin babu al’ummar da za ta samu cigaba muddin akwai kyama da nuna kiyayya ga junansu, wanda rashin hadin kai kan haddasa rashin fahimtar juna.
Shugaban yace akwai bukatar yin addu’o’i ganin babban zaben 2023 na gabatowa, don rokon Allah ya bada shugabanni na gari. ” Mu yarda da Allah mu sauke nauyin da ke kan mu na yin addu’a dan samun zaman lafiya da yin zaben shugabannin da za su samar da shugabanci na adalci wanda zai canja irin yanayin da muke ciki a yau saboda bunkasa rayuwar matasan mu masu tasowa.
Mun umurci shugabannin da ke jagorantar majami’u da su dauki fadakarwar mallakar katin zabe (PBC) da muhimmanci, su fadawa jama’a cewar su yi hakuri da duk yanayin da za su samu kan su wajen karban katin zaben da ma lokacin gudanar da zaben, ba za mu gushe ba sai mun tabbatar jama’a sun fito dan yin zabe a lokacin gudanar da babban zaben mai zuwa.
Yace mabiya addinin kirista na kallon zaben 2023 a matsayin wata hanyar samar da sabuwar Nijeriya, wanda muna kyautata zaton Allah na duban yanayin da kasar nan ke ciki kuma zai yi anfani da wannan lokaci na kawo sauyi a kasar nan. Dan haka mu fito mu zabi cancanta domin Allah na son kasar nan ta cigaba.
” Ina kira ga shugaban hukumar zabe ta kasa da mukarrabansa, da su ji tsoron Allah su yi aiki akan dokar da ta samar da su, su kaucewa aiki da son zuciya su tabbatar kasa su ke yiwa aiki ba wasu gungun jana’a ba.
A wannan shekarar ta 2023, mu yi anfani da ita wajen kawar da bambancin addini, kabila ko jam’iyya, mu hada kai dan nuna kishin kasa, wajen tabbatar da mun zama ‘yan kasa na gari ta hanyar sauke nauyin amanar da ke kan mu. Duk inda muka samu dama a aikin gwamnati ko wani wuri mu guji aiki da son zuciya wajen tara abin duniya, domin a lokacin da ka samu damar yin barna kuma ka hana shaidan damar shiga cikin lamarin lallai ka tabbata dan kasa na kwarai, saboda haka shekarar 2023, shekara ce ta gaskiya, hadin kai, kishin kasa da kauna ga abokan zama.
Alhaji Muhammadu Turaki, masanin kiwon lafiya ne kuma dan siyasa. Na ganin samar da shugabanni na gari a lokacin zaben 2023, shi zai tabbatar da gaskiyar ‘yan Nijeriya na samun cigaba musamman dan fita kuncin rayuwar da 2022 ta haifar.
Mun shigo sabuwar shekara da rauni a zukatan mu na talauci, yunwa da fatara, rashin tsaro da rashin cigaban kasa A wannan shekarar ya kamata mu fahimci cewar dole mu samar da sauyin da zai yiwa kasa anfani ta hanyar yin abinda ya dace.
” Matasan mu na bukatar karatun ta natsu ta hanyar samun madogarar rayuwa domin muna tsammanin su zama manyan gobe, idan yau din su ba tai kyau lallai za mu wayi gari cikin nadama da danasni, shugaban shekarun za su yi ta tafiya ba wani cigaban da aka samu.
Shekarar 2022, ta koyar da mu darussa da dama, muna fatar a wannan sabuwar shekarar za mu dauki matakin gyara da hannunwan mu.
Malam Adamu Aliyu Muhammed, malamin makarantar faramare a karamar hukumar Katcha ta Jihar Neja. Yace shekarar 2022 shekara ce da ba za mu manta ta ba saboda irin wahalhalun da al’umma shuka sha a cikinta. Muna bukatar a wannan sabuwar shekarar shugabanni za su kara kaimi wajen sauke nauyin da ke kan su musamman bangaren ilimi, samar da inganci rayuwa ga ‘yan kasa, domin musamman mutanen karkara na bukatar ganin sauyin rayuwa ta hanyar samar masu da tsaro, hanyoyi, da bunkasa ayyukan su.
Mun ji shugaban kasa ya saka hannu a kasafin kudin bana wanda ba a taba gabatar da irinsa ba a kasar nan, muna kyautata zaton idan za a aiwatar da abubuwan yadda aka tsara su a wannan shekarar za a samar da sauye sauye masu anfani ga kasa.
Muna bukatar hadin kai, zaman lafiya dan bunkasar ilimin ‘yayan talakawa da shekarar 2022 ta zame mana kunci, fargaba da tashin hankali. Dole shugabanni da al’umma su yi abinda ya dace dan kawo karshen matsalolin da kasar nan ta samu kanta a baya.
Jihar Bauchi
Shi kuma Gwamnan Jihar Gombe a sakonsa na sabuwar shekara kira ya yi ga al’ummar Nijeriya da su rungumi hakuri, jajircewa da fata na gari domin rayuwa ta kyautatu.
Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi kira ga al’ummar jihar da ‘yan Nijeriya baki daya su yi waiwaye tare da dabbaka darusan da suka koya a 2022 ta kowane fanni na rayuwa a sabuwar shekara ta 2023 tare da juriya, da sabunta fata.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnan ke bayyana fatan cewa sabuwar shekarar da aka shiga za ta kasance cike da farin ciki da wadata ga Jihar Gombe da Nijeriya baki daya.
A sakonsa na sabuwar shekara dauke da sanya hannun Ismaila Uba Misilli, Babban Daraktan Yada Labarun Gwamnan Jihar Gombe, gwamnan ya bukaci al’ummar jihar su kyautata fata tare da tabbatar da zaman lafiya da hadin kai don samar da tsaro da ci gaban jihar da kasa baki daya.
Ya yabawa irin juriya da jajircewar al’ummar jihar yayin fama da matsalolin zamantakewa dana tattalin arziki a shekarun da suka gabata sakamakon barkewar cutar Korona da yakin Rasha da Ukraine da kuma rashin tsaro da ake fama da shi a Najeriya, yana mai kira ga ‘yan kasar da kar su fidda rai, amma su ci gaba da kyautata fata da jajircewa.
Ya ce, “Shekara ta 2023 tana kunshe kyakkyawan fata a gare mu baki daya. Shekara ce mai muhimmanci da a cikin ta za mu sake fitowa zabe don zaben shugabannin mu a matakai daban-daban.
“Don haka yayin da muka shiga wannar sabuwar shekara, ina kira gare mu, mu yi koyi da darasin da muka koya a 2022 ta kowane fanni na rayuwa, mu ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da zaman lafiya, tsaro da ci gaban jihar mu mai albarka”.
Gwamna Inuwa yace duba da himmatuwar gwamnatin sa wajen samar da masana’antu, da samar da yanayi mai kyau na gina muhimman ababen more rayuwa da zamantakewar al’umma don cimma muradun su, Gombe ta hau kan kwakkwarar turbar ci gaba da bunƙkasar tattalin arzikin.
Gwamna Inuwa ya gode wa al’ummar jihar bisa addu’o’i da goyon baya da hadin kai da suke bawa gwamnatin sa, yana mai bukatar su, su ci gaba da gudanar da yin hakan don karfafa nasarorin da aka samu da kuma cimma buri da muradun al’ummah baki daya.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin wasu ‘yan Nijeriya dangane da fatansu na sabuwar shekara inda mafi yawansu suka yi addu’ar Allah sa a yi babban zaben 2023 lafiya.
Malam Nura Muhamad wani mazaunin Jihar Kano ne ya shaida mana cewa, “Babban fatanmu a wannan shekarar shi ne Allah ya zaba mana shugabanni na kwarai. Ka san a wannan shekarar ne za a yi babban zabuka a kasar nan. To, idan da za mu samu shugabbani na kwarai kuma a yi zaben nan lafiya kusan za mu iya cewa matsalolin mu sun kusan kawowa karshe. Don haka babbar fatarmu kenan.
“A fege guda ina da fatan cewa za a samu raguwar matsalar tsaro, da yake muna fama da matsalar rashin tsaro, don haka muna rokon Allah ya sa wannan sabuwar shekarar za ta zo mana cikin aminci da salama tare da kawo karshen matsalolin tsaro.”
Ita kuwa Hajiya Amina Salisu daga Jihar Bauchi, fatan dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali ta yi wa kasar nan, ta kuma jawo hankalin yara dangane da shiga bangar siyasa.
A cewarta, “Sai da zaman lafiya da kwanciyar hankali za a cimma kowace irin nasara a rayuwa. Don haka ina da fatan cewa a wannan shekarar za a samu kwanciyar hankali sosai, muna addu’ar Allah kawo tsaro da wadata. Dangane da babban zaben 2023 kuwa, fatanmu shine Allah sa a yi lafiya a kammala lafiya.
“Zan yi amfani da wannan damar na gargadi matasa da kada su bari a yi amfani da su wajen bangar siyasa da dabanci, yin hakan ba ya taimaka wa kasa ta kowace fuska. Muna fatan za a samu wadatar tattalin arziki da kiwon lafiya a sabowa shekara,” ta shaida.
Dakta Ibrahim Ibrahim Inuwa, maida hankali ya yi ta fuskanci tattakin arziki da cewa, “Idan ka kalli halin da kasar nan take ciki a yau abun tsoro ne. Dubi bashin da ke kan kasa da irin rashawar da ake tafkwa a kasar nan. Don haka idan ba a yi hankali ba nan gaba sai an rasa yadda za a tafiyar da lamura a wannan kasar.
“Don haka fatanmu shine a samu yanayin dakile rashawa da cin hanci a 2023 ta yadda tattalin arziki zai habaka ya samu ingatuwa. Kuma a samu yanayin taimaka wa talakawa da masu karamin karfi cikin al’umma.”
Murtala Adamu fatan samun sauki rayuwa ya yi, “Fatanmu shine jama’a su ji tsoron Allah su koma ga Allah.
Yawancin matsalolin da suke faruwa a kasar nan na da alaka da sabon Allah da mutane ke yi. To muna fatan a sabon shekarar nan al’ummar kasar nan za su ji tsoron Allah domin samun rayuwa mai sauki kuma mai inganci.
“Sannan muna addu’ar Allah zaba mana shugabanni na kwarai daga kowace matakai.
Ya kamata zuwa yanzu al’ummar Nijeriya su mance da siyasar jam’iyya su nemi cancanta, a kowace jam’iyyar mutum na kwarai ya fito a mara masa baya domin ta hanyar samun shugabanni na gari ne za a samu shugabanci na kwarai da tafiyar Mulki cikin adalci da kwanciyar hankali. Amma idan muka cigaba da kuskuren da muke yi na yin zabe don kudi to tabbas za mu cigaba da zabo tumun dare wadadan za mu zo mu yi danasanin zabinsu.
“Ga mata da matasa da ake ba su dan taso sisi a yi amfani da su wajen tafiyar da lamuran siyasa ta hanyoyin da basu dace ba, ya kamata su yi karatun ta nutsu su daina domin rike mutuncinsu da kimarsu.”
Kazalika, wani mazaunin Jihar Zamfara, Muhammad Hashimu, ya bayyana cewar ba su da fatan da ya wuce zaman lafiya ya samu karbuwa sosai a yankin domin suna cikin matsala ta masu garkuwa da mutane fa fashi da makami.
“Mu al’ummar Zamfara da jihohin da ke kewaye da mu, fatanmu a wannan shekarar shine a samu shawo kan matsalolin masu garkuwa da mutane da ‘yan fashin daji domin kyautata zamantakewar mutane a kowani lokaci.”