Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ƙaddamar da bincike game da mutuwar wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, da wasu matasa suka fusata suka far masu inda a ƙarshe suka kashe su, a garin Daga da ke ƙaramar hukumar Jibiya a jihar Katsina.
Rahotanni sun bayyana cewa waɗ anda ake zargi da aikata fashi da makamin sun kai wani samamaye ne a gidan wani mutun mai suna Abdulmumini Daga da kuma wasu mutane uku.
Kazalika binciken ya nuna cewa mutanan garin Daga ne suka sami labarin shigowar ɓarayin, inda nan da nan suka baza mutanan su domin yin kwanton baina kuma suka hallaka su.
Ya ƙara da cewa lokacin da jami’an ‘yan sanda suka isa inda abin ya faru sun tarar matasan da suka fusata har sun ɗ auki doka a hannu, amma dai ‘yan sanda sun yi nasarar samun bindiga kirar AK47 da kuma harsasai masu rai.
DSP Gambo Isah ya bayyana cewa tuni suka ɗ auke gawawakin waɗ anda aka kashe zuwa asibitin gwamnatin tarayya da ke Katsina inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.
Idan za’a iya tunawa mutanan garin Jibiya da kuma Magama jibiya sun sha kokawa game da yadda ake yawan kai masu hare-hare ba ji ba gani, tare da garkuwa da jama’a sai an bada kuɗ in fansa.
Al’amarin da jami’an ‘yan sanda suka bayyana cewa suna iyakar koƙarinsu na ganin sun shawo kan wannan babbar matsala da ta addibi wannan yanki da ake tinkaho da shi ta fuskarcin kasuwanci.