Jami’ar Jihar Kogi ta bayyana damuwa kan mutuwar wani malamin jami’ar da aka same shi da wata ɗaliba a cikin ɗakin wani otal da ke unguwar Felele a birnin Lokoja.
A cikin wata sanarwa, jami’ar ta ce mutuwar abin baƙin ciki ne kuma tana aiki da rundunar ’yansanda don binciko musabbabin faruwar lamarin.
- Dalilin Ciwon Baya Yayin Goyon Ciki Da Hanyar Magance Shi
- Jami’ar Ilorin Ta Karrama Shugabannin JAMB, THISDAY Da Wasu 63 A Bikin Shekara 50
Sai dai jami’ar ta nesanta kanta daga jita-jitar da ke yawo cewa Lubabat Bello ce ke da hannu cikin lamarin, wadda aka same ta a ɗakin lokacin da jami’an tsaro suka isa wajen.
Jami’ar ta nemi jama’a da su dakata da yanke hukunci kafin fito da sakamakon binciken da hukumomi ke yi.
Ta kuma buƙaci jama’a su kwantar da hankali tare da bayar da haɗin kai domin a gano gaskiyar abin da ya faru.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp