Mu’ujizozin Annabi Muhammadu (SAW); Karatu Na Hudu

Tare Da Sayyadi Ismail Umar Mai Diwani

A uzu billahi minas shaidanir rajiym. Bismillahir rahmanir rahim. Wa sallallahu ala Nabiyyil Karim. Alhamdu lillah, masu karatu a yau za mu ci gaba da karatun Darasin da muke yi a ‘yan makwannin da suka gabata game da Fifikon da Allah ya yi wa Annabi Muhammadu (SAW) a kan sauran Annabawa da Manzanni. Idan ba a manta ba, muna cikin kawo Abubuwan da Allah ya yi wa Annabi Ibrahim (AS) amma kuma aka bai wa Annabi Muhammadu (SAW) su; ba kuma tare da ya roka ba, har kuma aka kara masa da wasu abubuwa fiye da na Annabi Ibrahim (AS). A yau ma za mu ci gaba daga inda muka tsaya.

Allah ya fada mana a cikin Alkur’ani cewa, Annabi Ibrahim ya roki kar Allah ya kunyata shi ranar tashin kiyama. “Allah kar ka kunyata ni ranar tashin kiyama”. Allah ba zai kunyata Annabi Ibrahim (AS) ba ranar tashin kiyama, Allah ya riga ya karbi addu’arsa. Amma Allah bai fada mana Annabi Muhammadu (SAW) ya fadi wannan ba, duk da dai mun san Annabi yana neman gafara. Sai kuma Allah ya ba shi, inda ya ce “ranar tashin kiyama rana ce da Allah ba zai kunyata Annabi (Muhammadu SAW) ba, da wadanda suka yi imani tare da shi”. Ka ga abin da Annabi Ibrahim (AS) yake kwadayi kuma ya roka ga shi an ba Annabi Muhammadu ba tare da ya roka ba, ba ma shi kawai ba har da wadanda suka yi imani tare da shi duk an ba su abin.

Haka nan Annabi Ibrahim (AS) ya roki Allah ya sanya masa yabo da shaida mai kyau a wurin bayinsa, ya ce “Allah ka sa a yi mun shaida mai kyau har karshen duniya”. Za ka ga Yahudu da Nasara in suna wa’azinsu suna bata wasu Annabawa amma shi kuwa Annabi Ibrahim kowa yana cewa nasa ne, Yahudawa sun ce nasu ne, Nasara sun ce nasu ne, Maguzawa ma na Makka masu bautar gunki su ma sun ce nasu ne. Amma Allah ya ce duk ba nasu ba ne. A cikin Alkur’ani Allah ya ce Ibrahim bai kasance Bayahude ba ko Banasare, illa cewa dai shi na Annabi Muhammadu (SAW) ne Musulmi, haka nan kuma Mushirikan Makka Annabi Ibrahim ba naku ba ne.

Annabi Ibrahim ya roki Allah kowa yana yabonsa. Amma shi kuwa Annabi Muhammadu (SAW) bai roka ba, sai ga shi Allah ya ce masa “Mun daukaka ambatonka”. In dai za a kira Allah da Ubangidantaka, to za a kira Manzon Allah (SAW) da aike na Manzanci (kamar dai yadda muka kawo bayanai game da haka a darasinmu na baya). Har gaba da Abadan, in dai za a ce Allah sai an ce Annabi Muhammadu (SAW).

Haka nan Annabi Ibrahim ya roki Allah ya kiyaye shi ya nesanta shi da iyalinsa ga bautar gunki. “Allah ka kiyaye ni da iyalina ga barin bautar gunki”, kamar yadda ya zo a cikin Alkur’ani. A nan, Annabi Ibrahim (AS) gunki kadai ya fada, amma shi kuwa Annabi (SAW) Allah ya ce duk wata kazanta ma ya kiyaye shi da iyalan gidansa (SAW). Kamar yadda ya zo a Alkur’ani, Ubangiji ya ce Allah yana nufi ne ya tafiyar da kazanta daga barin ku iyalan gidan (Ma’aiki). Kalmar “Rijsu” tana nufin duk wata kazanta ta bautar gunki da laifuka. Allah ya fade su kamar haka: giya, da caca, da gumaka da kyamaren gunki dukkansu kazanta ne da Allah ya kiyaye iyalan gidan Manzon Allah (SAW) ga barin su. Don haka kalubale ga wanda zai rika kirkiran wadannan yana dangana wa iyalan gidan Manzon Allah (SAW). Domin Allah duk ya tsarkake su a kan wadannan. Ka ga yanzu abin da Annabi Ibrahim (AS) ya ji tsoro ya nemi tsari da shi tare da iyalansa, Allah ya bai wa Annabi Muhammadu (SAW) har da kari. Bayan ma Allah ya ce zai kiyaye su ga barin kazantar sai ya kara da cewa zai tsarkake su (iyalan gidan Manzon Allah SAW) tsarkakewa (kila Ma’arifa, kila kuma wata magana ce mai tsawo).

Bayan wannan, Annabi Ibrahim (AS) lokacin da aka kama shi za a jefa shi a cikin wuta, wuridin da ya rika yi shi ne “Hasbiyallahu wa ni’imal wakil (Ma’ana Allah ya ishe ni”. Shi kuwa Annabi Muhammadu (SAW) Allah ne yake masa. Allah ya ce, “Ya kai wannan Annabi, Allah ya ishe ka (ya isar maka)…” wai a bari ma ya nema ya fada da bakinsa ba a bari ba, Allah da kansa ya fada masa cewa ya isar masa saboda gatansa a wurin Allah (SAW). Malamai suka ce wannan kadan kenan daga bambancin da ke tsakanin “Khalilu (Badade)” da “Habibu (Masoyi”.

Sannan a wani misalin kuma, Allah Ta’ala ya bai wa Annabi Ibrahim iko ya karairaya gumaka. Shi ma Annabi Muhammadu (SAW) Allah ya ba shi hakan. A ranar Fatahu Makkata, Manzon Allah ya karya gumaka 313 da ke cikin Ka’aba da kewayenta. Shi Annabi Ibrahim (AS) gatari ya sa ya karya, shi kuwa Manzon Allah kwagiri (sanda) ne a hannunsa, idan ya nuna gunki ta keyarsa sai ya fadi ya ci ta goshi, idan kuma ya nuna shi ta goshi sai ya fadi ta keya. A cikin wadannan gumaka da Manzon Allah ya rika nunawa suna karairayewa, wani an gina tushensa da darma, wani da karfe, wani da azurfa amma saboda Mu’ujizar Manzon Allah (SAW) da ya nuna gunki ya ce “ja’al hakku wa zahkal badil….” Sai ya fadi kuma a gaban mutanen Makka. Duk wannan yana daga cikin bambancin Badade da Masoyi a wurin Allah (SWT).

Wakazalika, Annabi Ibrahim (AS) shi ne Allah Tabaraka wa Ta’ala ya sa ya gina mana Ka’aba, ga ta nan har yau muna kewayawa na dawafi da komai Sunnar Annabi Ibrahim. Ga kuma su Safa da Marwa. To shi kuma Manzon Allah (SAW) sai da ya zamo yana da girma a cikin sha’anin Ka’abar nan. Manzon Allah yana mai shekara 25 kuraishawa sun sake gina Ka’aba, bayan sun kammala aiki sai kuma rigima ta kaure a tsakaninsu a kan waye zai dora Dutsen Hajarul Aswadu a inda yake (Dutsen da ake ce wa ‘shan nono’ a yayin dawafi). To kowace kabila tana tutiya da cewa ita ce mai girma ai kakanta ne wane, har abin ya kai ga zazzare takubba, sai Dattijai a cikinsu suka ce a’a ba haka (yaki) za a yi ba. Yadda za a warware rigimar ita ce a zabi manyan gari su kwana a masallaci, kar a fada wa kowa illa kawai a sa ido, duk wanda ya fara shigowa cikin masallacin nan gobe kafin rana ta fito shi ne zai yi musu hukunci. Idan ma ya ce shi ne zai dora musu Dutsen sun yarda. Dattijan nan suka kwana a masallaci, sai ga shi da sassafe Annabi Muhammad (SAW) shi ne ya fara shigowa cikin masallacin, duk gabadaya suka ce sun yarda da Amintacce (Amin) ya yi musu hukunci. Suka fada masa abin da suke so, Manzon Allah ya ce ai wannan mai sauki ne, ya shimfida mayafinsa, ya ce kowane gida (kabila) suka kawo babban cikinsu, Manzon Allah ya ce kowa ya kama mayafin, suka kama aka daga Dutsen, sai da aka kusa dab da inda za a jiye Manzon Allah ya sa hannunsa mai albarka ya dauka ya sa shi a inda ake so. Wannan duk yana daga cikin girman Masoyi (Manzon Allah SAW) a kan Badade (Annabi Ibrahim AS) a wurin Allah.

 

Exit mobile version