Na Ba ’Yan Adawa Kunya

Mai koyar da yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal, Arsene Wenger, dan asalin ƙasar faransa ya ce ya rufe bakin masu sukarsa sau biyu a jere da ake fara zura musu ƙwallo a raga a wasa daga baya kuma su farke su yi nasara a ƙarshen wasan.

Arsenal ta yi nasarar doke Swansea City da ci 2-1 a gasar Premier wasan mako na 10 da suka yi a ranar Asabar ɗin data gabata kuma Swansea ce ta fara zura ƙwallo a raga.

Wenger ya ce Arsenal ta saka ƙwazo bayan da aka zura mata ƙwallo ta farke ta kuma yi nasara a ƙarawa da Swansea da kuma Eɓerton a gasar firimiya da Norwich city a gasar cin kofin Caraboa.

Mista Wenger, wanda ya ja ragamar Arsenal wasa na 800 a ranar Asabar ya kuma ce sun nuna ƙwarewar lashe wasa, musamman ace kai aka fara zurawa ƙwallo a raga ka farke sannan kayi nasara.

Wenger ya ƙara da cewar ya kunyata masu sukarsu tun a wasan Eɓerton da Norwich da kuma wanda suka yi da Swansea saboda haka nan gaba sais u nemi wani abin da zasuyi suka akai.

Wenger ya ci gaba da cewa dagewa da sadaukarwar da yan wasan ƙungiyar suke nunawa shine yasa suke samun nasara a wasannin da suke bugawa a yan kwanakin nan.

Sai dai yace zaiyi gyara a yanayin tsayuwar yan wasansa na baya domin bai kamata ace wasanni uku su ake fara zurawa ƙwallo a raga ba.

 

Exit mobile version