Na Dawo Chelsea A Matsayin Kwararre – Lukaku

Lukaku

Sabon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Romelu Lukaku, ya ce ya sake komawa Chelsea a matakin kwararren dan wasa, tun bayan kakar wasa biyu rabon sa da Premier League.

Lukaku, mai shekara 28 ya koma Chelsea daga Inter Milan a makon jiya a kan kudi fam miliyan 97.5 a karo na biyu da zai buga mata wasa, bayan zaman da ya yi tsakanin 2011 zuwa 2014.

“Yanzu ne nake cikakken dan kwallo kuma na tanadi dukkan kwarewar da mai cin kwallaye ke bukata a wasanni, zan kuma kara kwazo a fannin da nake da rauni a sabuwar kungiya ta.” in ji Lukaku.

Lukaku dai shi ne dan wasan da Chelsea ta saya mafi tsada a tarihi, kuma na biyu a tsada a Birtaniya, bayan Jack Grealish da Manchester City ta dauka daga kungiyar kwallon kafa ta Aston Billa a bana.

Dan wasan tawagar Belgium shi ne kan gaba a ci wa Inter kwallaye mai 24 a Serie A a kakar da ta wuce da kungiyar ta lashe kofin a karon farko tun bayan shekara ta 11 bayan da ya bar Chelsea, Lukaku ya buga wasannin aro a Eberton daga nan kungiyar ta saye shi, ya koma Manchester United a shekarar 2017.

Dan kwallon ya yi kakar wasa biyu duk da magoya bayan Manchester United ba sa kaunarsa da cewar ya yi nauyi sannan bashi da kuzari amma kuma Lukaku bai buga wa Chelsea karawar da ta doke Crystal Palace 3-0 ranar Asabar a wasan makon farko a gasar Premier sai dai watakila ya fara yi wa Chelsea wasa a karawar da za ta yi da Arsenal ranar Lahadi.

Exit mobile version