Shafin ADABI shafi ne da ke zakulo muku fasihai kuma hazikan marubuta, manya, da kanan, haka kuma shafin na kawo muku sharhin wasu litttafai dominku masu karatu. A yau shafin na tafe da fasihiya, hazikar marubuciyar littafin Hausa, wato FATIMA ZAHRA MAZADU wadda aka fi sani da PRINCESS MAZADU a fannin rubutu. Ta bayyana wa masu karatu
Ya cikakken sunan Malamar?
Sunana Fatimah Zahra Mazadu.
Masu karatu za su so su ji dan takaitaccen tarihinki.
Ni haifaffiyar garin Gombe ce bafulatana, nayi firamare, sakandare, jami’a, duk anan Gombe, a takaice dai ni marubuciya ce.
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma rubutu?
Tsari, jin dadin karantawa, da son bayyana tawa basirar dan jama’a su amfana, tun ina karama in na ji wani shiri na abokin hira rediyo na gombe kamar nike Rubutun, abun na min dadi yadda ake cewa wai wasu masu basira da kwanya ke rubutawa, Alhamdu lillahi na gwada kuma na ji dadi.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
Ah! gaskiya na sha, dan na fara da zama a ‘Gorgeous’, Kainuwa, Sannan na yi ta gwagwarmaya da Umar Dalha Funtuwa da sauran masoya muka yi tsayin daka muka kafa ‘Golden Pen Writers Association’.
Ya batun iyaye lokacin da ki ka fara sanar musu cewa kina son fara rubutu, shin kin fuskanci wani kalubale daga gare su ko kuwa?
Ban samu ba dan yawancinmu a kan masu basira da ilimi ke rubutun, sannan kuma karuwa ce da kara wayar da al’umma, so ni gaskiya hadin kai ma na samu.
Ya farkon fara rubutun ya kasance?
Gaskiya na sha gyara da jin nauyin Rubutun.
Daga lokacin da kika fara kawo yanzu kin rubuta labari kamar guda nawa?
Na rubuta sun kai kamar biyar.
Cikin labaran da kika rubuta wanne ki ka fi so wanda ya zamo bakandamiyarki?
Abun da yake raina.
Wanne labari ne lokacin da ki ke rubutawa ya fi ba ki wahala, kuma me ya sa?
Sirrin da ke raina, saboda ya dauko yawa ya gajiyar da ni.
Cikin labarin da ki ka rubuta, akwai wanda ki ka buga ko ki ke saka ran bugawa?
Ban taba bugawa ba.
Wanne irin Nasarori ki ka samu game da rubutu?
Alhamdu lillahi da yawa, na san mutane, wasu da yawa sun san Fatimah Mazadu ko in ce Princess Mazadu.
Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta game da rubutu ko ga masu karatu?
A’a ban taba fuskantar kalubale ba.
Ya kika dauki rubutu a wajenki?
Abu mai mahimmanci.
Wanne irin labari ki ka fi maida hankali a kai wajen rubutawa?
Na Soyayya da Tausayawa.
Mene ne burinki na gaba game da rubutu?
Zamowa babbar marubuciya sananniya.
Ko akwai wanda ya taba bata miki rai game da rubutunki ko aka yaba?
Ba a taba bata min ba, ana yabawa dan ‘Abun Da Yake Raina’ ya yi farin jini sosai.
Wanne abu kike tunawa har ki ke jin dadi game da rubutunki?
Alkalamina.
Bayan rubutu kina wata sana’ar ne?
Ma’aikaciya ce ni, kuma ‘yar makaranta dan a yanzu haka karatu nake karawa, shi ya dan dakata da ni daga rubutu.
Kafin karatun ya ki ke iya hada aikinki da rubutunki
Toh abun sai godiya dan akwai wahala kam.
Kamar da wanne lokaci kika fi jin dadin yin rubutu?
Da Sassafe ko Dare.
Me za ki ce da makaranta labarinki?
Ina son su ina kaunar su, kuma kar su manta da Princess Fatimah Mazadu, har abada ina son su ina kaunar su duk inda suke a fadin duniyar nan.
Gaida mutum biyar
Umar Dalha Funtua, Hadiza D. Auta, Ummi Yusuf, Anup Janyau, Rabi’at Sidi Bala (Big girl). Kune jinin jikina ina ji da ku har abada, na san muhimmancinku da rawar da ku ka taka a rayuwata.