Shafin ADABI shafi ne daya saba zakulo muku fitattun marubuta littattafan hausa har ma da masu tasowa domin jin ta bakinsu game da abin da ya shafi rubutunsu.
A yau ma shafi na tafe da wata bakuwar marubuciyar wato; MARYAM FARUK wacce aka fi sani da UMMU MAHEER inda ta bayyanawa masu karatu batutuwa masu yawan gaske da suka shafi rayuwarta da kuma rubutunta. Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu AISHA IDRIS ABDULLAHI (ALEESHAT) Kamar haka;
Wane labari ne ya zamo bakandamiyarki?
Wata Kishiyar.
Wane labari ne ya fi baki wahala wajen rubutawa?
A cikin rubutuna wanda ya fi ba ni wahala shi ne; MATAR MUTUM. Dalili; labarin ya kunshi ‘characters’ da yawa masu mabanbantan halaye. da yawan marubuta sukan rude a rubutu har ta kai sukan canza dabi’un jarumai idan tafiya tayi nisa ba tare da saninsu ba. Akwai bukatar nutsuwa sosai. A sanda nake rubutun wani sa’in sai na koma nayo karatun baya a kokarin ganin komai ya tafi mun daidai ba tare da na canza akala ko na shigar da abun da babu shi a halayyar wani ba hakan ya sa rubutun bai yi mun sauri ba ga kuma tarin makaranta dake dakon jiransa a kullum.
Wane irin nasarori ki ka samu game da rubutu?
Alhamdulillah. Ta dalilin rubutu na hadu da mutanen kirki wanda ba dan rubutu ba babu lallai in sansu a rayuwata. Rubutu ya ba ni sababbin iyaye, yayye, kanne, kawaye har da aminai. Rubutu ya kai sunana inda ni ban je ba ciki da wajen kasar nan Alhamdulillah.
Wane abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ki taba mantawa da shi ba game da rubutu?
Abin farin ciki yanda mutane suke kirana a waya su yi mun addu’a da fatan alkhairi akan yadda rubutu na ya shafi rayuwarsu ya kuma haska musu mafita cikin wani abu daya damesu yana matukar saka ni farin ciki.
Kin taba kuka sanadiyyar rubutu ko karatu?
A dabi’ance dama ni mutum ce me saurin kuka, sannan salon rubutuna ina yinsa yanda makaranci zai ji tamkar a gabansa koma a karankansa abun da yake karantawa yake faruwa. A sanda nake rubuta littafin MATAR MUTUM episode din rasuwar AHMAD BECHI sai da nayi sati a kullum na dauki abin rubutu zan fara sai in kasa kukan tausayin al’amarin ya hanani haka bayan da nayi ‘publishing episode’ din har sai da na ji kamar in gogeta daga cikin littafin saboda yadda ta famawa mutane da yawa mikin rashin makusantansu. Tamkar gaske haka muka yi kukan rashin Ahmad sai da muka shafe kwanaki muna zaman makoki kafin muka ci gaba.
Kamar wane lokaci ki ka fi jin dadin yin rubutu?
Na fi jin dadin rubutu da rana bayan na gama ayyukan gida na gaji saboda ban iya baccin rana ba dan haka sai in yi amfani da wannan lokacin nayi rubutu, wani lokacin na kan yi da daddare sai dai nafi jin dadi da rana gaskiya.
Bayan rubutu kina yin wata sana’ar?
Ina kasuwanci sannan ina koyarwa, karfe sha daya nake shiga makaranta na tashi karfe biyu, dan haka a ranakun makaranta kafin na fita nake yin duk wani aikin gida kasuwnaci kuma a cikin gida ne ina siyar da kayayyakin sakawa dana amfani kusan duk abin da nake bukatar siya ta waya ne zan zaba a kawo mun duk da akwai abubuwan da suke bukatar dole sai naje kasuwa da kaina kamar idan zan yi hijabai nafi so in je in zabo yadi da kaina.
Wacce marubuciya ce take burge ki tun kafin ki fara rubutu?
Anti Fauziyya D. Sulaiman ita ce ‘role model’ dina a rubutu, kuma har yau Allah bai saka na taba magana da ita ko na ganta a zahiri ba.
Wace ce babbar kawarki a marubuta?
Suna da yawa.
Wacce shawara za ki bawa masu karatu har ma da sauran ‘yan’uwanki marubuta?
Shawarata ga makaranta shi ne; su ringa uzuri ga marubuta domin marubuta mutanene tamkar kowa idan har an ga wani kuskure ko ajizanci a maimakon a aibata mutum ayi kokarin yi masa uzuri tare da nuna masa kuskurensa ta hanyar daya dace. Sannan makaranta su ringa karatu domin daukan darasin dake ciki ba iya zallar nishadi ba. Duk abin da marubuci ya kawo yana da dalilinsa da kuma abin da yake son isarwa amma sauda yawa makaranta sukan kulle idonsu su ki karbar gaskiya muddin ba ta zo daidai da ra’ayinsu ko abin da suka so ya kasance ba. Ga ‘yan’uwana marubuta kuma mu tsaya akan gaskiya, mu sani duk abin da muka rubuta akwai ranar da zamu tsaya gaban ubangiji akansa. Ina kira ga masu rubutun batsa da su ji tsoron Allah. Ko basu bari dan goben kansu da ta ‘ya’yansu ba domin duk wanda ya lalace sanadiyyar abin da suka rubutawa hakkinsa ba zai barsu ba ga tarin zunubi da suke daukarwa kansu da fushin ubangiji bisa yada barna a doron kasa. Mu yi rubutun da ko bayan ranmu za a karanta ayi mana addu’a. Mu yi rubutun da ba za mu ji kunyar nuna shi a ko ina ba. Da yawan marubutan batsa suna boye sunansu kenan sun san abin da suke aikatawa ba me kyau bane wadanda kuma suka shahara a ciki ba sa kunya ba kuma sa tsoron Allah suke yada badala da sunan neman kudi to su ji tsoron Allah domin rayuwar duniya ba matabbaciya ba ce fatan kowacce musulmi yayi karshe me kyau. Allah ya datar damu
Me za ki ce ga masu karanta labaranki?
Ina gaida masoya rubutuna duk inda kuke a fadin duniyar nan ina kuma Alfahari daku. SON SO FISABILLILLAH
Me za ki ce da makaranta shafin Adabi har ma da ita kanta jaridar LEADERSHIP?
Ina gaida duk wanda yake karanta wannan hira tawa idan ka/kin kasance me bibiyar littattafaina ina miki/maka albishir da labarai dake tafe wanda suka zarce na baya dadi da ma’ana. Ga wanda basu taba karanta littattafaina ba ku gwada ina da tabbacin ba za ku yi nadama ba. Jaridar leadership Hausa ina matukar godiya ga wannan dama da kuka ba ni. Ubangiji ya ci gaba da daukaka ku ya kuma kare mu baki daya daga dukkan abin ki. Nagode kwarai Allah ya saka muku da mafificin Alkhairi
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Da farko ina gaida mahaifiyata ta Hajiya Ummu Usman, ina gaida maigidana Engineer A. Mainasara tare da yarana. Gaisuwar bangirma ga dukka masoyan rubutun Ummu-maheer musamman ‘yan groups dina na amana tun daga Rubutacciyar Kaddarah zuwa Wata kishiyar, Halin kishi da kuma Jama’ar Gidan BECHI kawayen Hajiya Binta da Afeeyah. Garkonin Ladies ko ince Shuwa Arabs kafataninku na gaishe ku musamman ‘yan aji uku Jaa, Ina gaida ‘yan’Uwana marubuta manya da yara tsofaffi da sababbi.