A makon da ya gabata ne mu ka sami tattaunawa da Shugaban masu sayar da goro, Alhaji Ibrahim Sawaba. Wannan hira dai mun yi ta ne dangane da yadda a ka yi ya sami kansa a harkar sayar da goro kuma mu ji da ma gada ya yi ko kawai dauka ya yi da rana tsaka. Ga dai yadda hirar ta kasance tare da Wakilin LEADERSHIP A YAU, HARUNA AKARADA:
Ta ya ka sami kanka a harkar sayar da goro?
A gaskiya daman tun asalinmu iyayena suna harkar safarar goro ne daga kano zuwa zuwa wurare daban-daban, kuma kaka ma ya yi, sannan babana yazo ya yi, kuma fataucin goran ne ya kai iyayena har maiduguri inda a can aka haife ni. A maidugurin ana daukar goron cikin jirgin kasa zuwa sauran yankuna.
Kamar kasashe nawa ne ka ke ganin suna noma goro?
Eh, gaskiya akwai goron kamaru, akwai kuma goran abirikos, akwai na gana, gini, da siraliyon wanda ake kawo shi kasar nan
Kamar yadda ka dade kana harkar goro, shin ya cinikin baya da yanzu ya ke?
Magana ta gaskia ita ce, a lokacin da kudin mu ke da martaba munfi jin dadin ciniki, amma gaskiya yanzu komai ya yi kasa, domin ada goro kwaya daya bai wuce Naira bakwai, to amma yanzu sai jaka days ko Naira tamanin.
A wasu lokotan sai a ganku a zauna kamar ba ku yi ciniki ba, ya abin ya ke?
Wannan ce babbar kasuwar goro a jihar Kano?
Eh, a gaskiya duk fadin kasar nan babu inda ya fi nan Jihar Kano kasuwancin goro, domin daga sassan daban-daban na cikin kasar nan a kan zo domin saya.
Kasuwannin goro za su kai kamar guda yawa a jihar Kano?
Ba su da yawa, akwai daya a nan Ujile, akwai kuma na Mariri-mariri inda a ke sayar da buhunhunan goro, masu kasawa kadan ne kawai.
Shin ku masu sana’ar goro kuna samun bunkasar arziki kuwa?
Ka san komai hawa hawa ne, wani lokaci zaka ga akwai babba akwai na tsakiya, akwai na kasa kuma, domin shi goro kamar dau she ana sayar da buhu wanda kudinsa ya kai Naira dubi dari da a shirin, akwai na talatin da biyar, akwai na saba’in da biyar, ka san goro daushe shi a jiye shi a ke yi ya zama daushe, sannan a sayar bayan shekara biyu inda ya kai ya zama daushe.