Connect with us

LABARAI

Nakasassun Jihar Gombe Sun Roki Alfarma A Ranakun Zabe

Published

on

Kungiyar mutanen da suke da nakasa ta kasa (NAPWD) ta yi kira da hukumar zabe mai zaman kanta, da cewar, ta fito da wani tsari na musamman wanda zai ba ‘yan kungiyarta dama ta su yi “Zabe ba tare da wata matsala ba”.
“Mambobinmu suna fuskantar matsaloli tare da wulakanci a ranakun zabubbuka, saboda yawancin su, dole ce tasa suka bar jefa kuri’ar saboda matsalolin da suke fuskanta.
“Muna son ita INEC ta yi wani shiri na musamman wanda zai ba ‘yan kungiyarmu dama su jefa kuri’a ba tare da wata matsala ba.”
Wannan ce hanya kadai da mambobinmu za su samu dama yin zabe kamar yadda sauran ‘yan kasa za su yi” Alhaji Ali Goro shi ne shugaban kungiyar reshen Arewa maso gabas, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya.
Goro wanda shi kansila ne yanzu a karamar hukumar Balanga jihar Gombe ya yi wannan kiran ne ranar Litinin a Gombe, inda ya bada shawarar cewar, ya dace a ba duk ‘yan Nijeriya dama, su jefa kuri’a idan dai har kasar na bukatar ayi damukaradiyya wadda take ta gaskiya.
Shugaban ya yi kira da ita hukumar zabe mai zaman kanta, ta sa mutane wadanda suke da nakasa, wajen shirya zaben 2019, saboda hakan zai ba su damar bada shawara, yadda ‘yan uwansu ba za su fuskanci matsala ba lokacin zaben.
“A shekaraun da suka gabata INEC tana mantawa da mutane irinmu lokacin da suke yin shirin zabe, muna ganin wannan ba ayi mana adalci ba, ba kuma shi ne damukuradiyya ba”.
Ya ce, hukumomin tsaro su rika yin adalci, ga mutanen da suke da nakasa a ranakun zabe, su kuma nuna fahimta da rashin kyama gare su.
Haka nan ma ya yi kira ga jam’iyyun siyasa suma su rika tunawa da nakasassu, lokacin da suke zaben wadanda za su tsaya takara, saboda hakan zai sa su ga ashe ba a mayar dasu saniyar ware ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: