Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC), ta shirya bai wa kamfanonin sadarwar kasar nan wa’adin kwanaki 30 don shawo kan duk wasu matsaloli da masu amfani da layuka da sauran hanyoyin sadarwa ke fama da su.
A cewar hukumar, idan mai amfani da layi ya mika korafinsa amma aka ki a saurare shi, zai iya sanar da ita bayan kwanaki 30, inda ita kuma za ta dauki matakin da ya dace.
- Dubban Mambobin Jam’iyyar APC Sun Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar PDP A Bauchi
- NDLEA Ta Bankado Hodar Iblis Da Aka Boye Cikin Abincin Jarirai
An dai bayyana hakan ne cikin wani sabon daftarin dokokin ayyuka na hukumar da aka dora a shafinta na Intanet.
Masu amfani da wayoyin hannu a Nijeriya dai sun jima suna korafi kan yadda kamfanonin layuka ke nuna halin ko in kula da korafe-korafensu.
Wannan dalili ne ya sanya da yawan abokan hulda da kamfanin shiga sabgar sauya layi daga wannan zuwa wancan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp