Daga Muh’d Shafi’u Saleh,
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta tsare mutum 57, ta kuma samu wasu 200 da laifin safarar miyagun kwayoyi daga watan Janairu zuwa na Disambar 2020, a Jihar Adamawa.
Shugaban hukumar a jihar Idris Muhammad, ya bayyana haka ga manema labarai a Yola, lobe kacin da yake bayanin ayyukan hukumar na karshen shekara, ya ce cikin mutanen sun hada da 56 mazaje da mace guda.
Ya ce “hukumar NDLEA na tsare mutum 57 hadi da mace guda, da wadanda aka daure kan bangarori da dama kama daga maiyin wata 8 zuwa shekaru biyar, mutanen da’aka yanke hukuncin shekarunsu ya kama daga 18-50, akwai shari’o’i 58 a kotu ana kanyi” inji Idris.
Ya ce “mutum 200 muka kama, ciki akwai mata bakwai, mun kamasu da miyagun kwayoyi kilogaram 2,083.369, wiwi kilogaram 1,839.338, kayayayyakin maye kilogaram 244.030” ya jaddada.
Haka kuma shugaban ya bayyana hanyoyin da su ke bi na fadarwa da wayarma jama’a kai game da illar shan miyagun kwayoyi, ya ce hukumar na gudanar da taron bita, shirye-shurye a kafafen sadarwa, da shirin da suke yi a NTA da nufin rage ta’ammuli da migayun kwayoyin.
Shugaban hukumar ya kuma kuka game da karuwar adadin mutanen da hukumar ta kame a shekarar 2020, da kuma kwanaki 10 farko Na watan Junairun 2021, ya ce hukumar kame mutum 42, dauke da miyagun kwayoyi kimanin kilogaram 11.431.
Muhammad Bello, ya kuma yaba da goyon bayan da gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri, ke baiwa hukumar, domin ganin yaki da shan miyagun kwayoyi ya cimma nasara a jihar.