Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a Jihar Bauchi, ta ce ta kama mutane 415 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi tare da kwato jimillar tan 1.2 na kwayoyi daban-daban a shekarar 2024.
Kwamandan NDLEA a jihar, CN Ali Aminu, ya bayyana haka yayin wata hira da manema labarai ranar Talata a Bauchi.
Ya ce, tsakanin watan Janairu zuwa Disamban 2024, hukumar ta samu nasarar kwato kwayoyi masu kamar su tabar wiwi, Diazepam, Edol-5, Pentazocine, Methamphetamine, Rohypnol, da Tramadol.
A cewarsa, hukumar ta gabatar da karar mutane 70 a kotu, inda an yanke wa mutane 84 hukunci, yayin da mutane 18 ke ci gaba da fuskantar shari’a a gaban babbar kotun tarayya da ke Bauchi.
Haka kuma, hukumar ta sauya tunanin masu amfani da miyagun kwayoyi 137 ta hanyar shawarwari karkashin kulawarta.
CN Aminu, ya yi kira ga jama’a da su guji ta’ammali da safarar miyagun kwayoyi, yana mai tabbatar da cewa duk wanda aka kama da laifin zai gurfana a gaban kotu.
Ya kuma nuna godiyarsa ga sauran jami’an tsaro bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen samun nasarorin hukumar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp